Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin tarayya ta sanar da wani sabon tsari da zai bai wa ɗalibai damar shiga manyan makarantu ba tare da wajibcin samun Lissafi ko Turanci a WAEC ko NECO.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da ma’aikatar ilimi ta Nijeriya ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Oktobar 2025.
Sabuwar dokar, wacce Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, CON, ya gabatar, ya ce, wani mataki ne shirin sabunta fatan al’umma da bai wa kowa damar samun ilimi.
Alausa ya ce, la’akari da cewa a kowacce shekara akan samu ɗalibai sama da miliyan 2 d ake zama domin rubuta jarrabawar JAMB (UTME), amma ɗaliba 700,000 ne ke samun gurbin karantu.
“Ba gazawa ce take sa ɗaliban rashin samun gurbin karatu ba facce wasu tsofaffin tsauraran dokoki shiga manyan makarantu waɗanda akwai buƙatar gyara su don yin adalci da bai wa kowa dama.
Ga yadda sabuwar dokar za ta kasance: Sabuwar dokar za ta shafi makarantun jami’o’i da na fasaha da kwalejojin ilimi da makarantun koyar da harkokin kasuwanci (IEAs) a faɗin ƙasar nan.
Jami’o’i: Tilas dalibi ya zama yana da kiredit 5 a darussan da suka shafi kwas ɗin da yake so ya yi da ya haɗa har da Ingilishi a sakamakon zaman jarrabawar da bai haura biyu ba. Lissafi zai zama wajibi ne kawai ga ɗaliban da ke fannin kimiyya da fasaha da kwasa-kwasan kimiyyar al’umm.
Makarantun Fasaha (ND Leɓel): Samun kiredit 4 a darussan da suka jiɓanci kwas ɗin da mutum zai yi cikin har da English ga wadanda suke karanta abin da ba kimiyya ba ne da kuma wajibcin Lissafi ga daliban kimiyya.
Makarantun Fasaha (Matakin HND): Samun kiredit biyar (5) ciki har da Ingilishi ga da Lissafi.
Kwalejin Ilimi (Matakin NCE): Samun kiredit 4 ciki har da Ingilishi ga ɗaliban Arts da kimiyyar nazarin al’umma da kuma lissafi ga ɗaliban Kimiyya da koyon sana’o’i da ‘yan ‘Technical’.
Kwalejijin Ilimi (Matakin B.Ed): Samun kiredit 5 ciki har da Ingilishi da Lissafi ga kwasa-kwasan da suka wajibta haka.
Makarantun koyar da sana’o’i (IEAs): za su yi amfani da tsarin makarantu fasaha ga masu ND. Sannan an soke Babbar Diploma (NID).
Sannan an sake fasalin diflomar harkokin masana’antu (NID) tare da maye gurbinta da babbar diflomar ta ƙasa (ND) don tabbatar da sahihanci da komai ya zama bai-ɗaya.
A yanzu hukumar NBTE na sake tantance dukkan makarantun IEAs a faɗin Nijeriya domin tabbatar da sun cika sharaɗin ND.
A cewar sanarwar, wannan gyara zai faɗaɗa da ba da damar samun gurbin shiga manyan makarantu ga dalibai 300,000 daga 250,000 a kowace shekara.
Mista Alausa ya ce, daidaita tsarin dokokin neman gurbin karatun zai taimaka wajen rage yawan matasan da ba sa zuwa makaranta da ƙarfafa samun horaswa na koyon sana’o’i da ƙwarewa wanda zai sa tsarin ilimin manyan makarantu a Nijeriya ya yi daidai da tsarin da ake da shi a duniya.
Ya jaddada aniyar gwamnati ma ganin matasa waɗanda su ne ruhin ƙasar sun samu duk wata.
