Amnesty ta nemi Tinubu ya soke yafiyar da ya yi wa waɗanda su ka aikata manyan laifuka 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Amnesty International ta bayyana damuwa kan afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a kwanan nan, inda ta buƙaci gwamnati da ta sake duba matakin.

A ranar Alhamis da ta gabata, Tinubu ya bayar da afuwa ta shugaban ƙasa ga ɗaya daga cikin jagororin da su ka kafa Nijeriya, Herbert Macaulay, da kuma tsohon ministan babban birnin tarayya a zamanin mulkin Babangida, Manjo Janar Mamman ɓatsa (ritaya), da Maryam Sanda da aka yanke wa hukuncin kisa sakamakon kashe mijinta da ta yi da sauran wasu mutane 172.

Sai dai wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce, kasancewar wasu daga cikin waɗanda suka amfana da afuwar sun hada da masu manyan laifuka kamar na miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, kisan kai da kuma wasu ‘yan ƙasashen waje.

Channels TV ta rawaito cewa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Amnesty ta bayyana matukar damuwa kan matakin Tinubu na bayar da afuwa ga wasu da aka samu da laifukan take haƙƙin ɗan Adam.

ƙungiyar ta ce wannan mataki ya fifita masu laifi akan waɗanda suka cutu da laifukan da aka aikata, inda hakan ya hana su samun adalci da diyya.

“Yadda hukumomin Nijeriya suka aiwatar da wannan tsarin afuwa kamar sun fi mayar da hankali kan waɗanda suka aikata laifuka maimakon samar da adalci da diyya ga waɗanda suka cutu da iyalansu,” inji ƙungiyar.

ƙungiyar ta gargaɗi cewa wannan hukunci zai iya raunana dokoki, hana bayyana gaskiya da ɗaukar mataki, da kuma kara ƙarfafa rashin hukunta masu laifukan take haƙƙin ɗan Adam a Nijeriya.

By ukarofi