Gwamnatin Katsina za ta kafa gidan rediyo na manoma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ma’aikatan gona Farfesa Ahmad Muhammad Bakori ya sanar da haka a hira da manema labarai kan ziyarar aiki da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima zai kawo a Katsina mako mai zuwa.

Mataimakin shugaban ƙasar zai kawo ziyarar aiki na kwana biyu inda zai jagoranci buɗe taron hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i SMSE ta ƙasa a Katsina.

Zai kuma ƙaddamar da wasu ayyuka na bunƙasa ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar.

Farfesa Bakori ya ce mazaunin gidan rediyon zai kasance a cibiyar kula da manoma da aka kammala gina wa, ana sa ran Kashim Shettima zai buɗe cibiyar.

Kwamishinan ya ce wannan cibiyar shine na farko a ƙasar da gwamnatin Katsina ta gina ,za ta rinƙa horas da manoma yadda za su fahimci yadda noma ya koma irin na zamani da kuma ilmantar da su kan abinda ya shige masu ido.

Sanata Kashim Shettima zai buɗe hanyar da ta tashi daga babban masallacin juma’a na fadar Sarkin Katsina zuwa makarantar kiddies ta miƙe har ruwa WTC a cikin garin Katsina.

Kwamishinan ayyuka injiniya Magaji Ingawa ya shaidawa manema labarai cewa hanyar mai tsawo kilomita 3.3 da gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 1.9 ya ƙunshi magudanan ruwa da fitillu masu amfani da hasken rana da aka kafa a hanyar wanda yana ɗaya daga cikin aikin da Sanata Kashim Shettima zai buɗe.

Haka kuma mataimakin shugaban ƙasar zai karrama wasu yan kasuwa na Jihar Katsina da su kai fice wajen tafiyar da harkokin kasuwancin su.

By ukarofi