Gwamna Lawal ya mayar da malaman makaranta 103 da aka kora bakin aiki

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da mayar da malaman makaranta 103 da aka kora don su koma makarantun da suke koyarwa ba tare da ɓata lokaci ba.

Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar, Alh. Wadatau Madawaki ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa a yau Juma’a.

A cewarsa, gwamnan ya umurci ma’aikatarsa da ta biya dukkan albashin su na watanni bakwai daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekara.

Madawaki ya bayyana cewa malaman da abin ya shafa na daga cikin malamai 780 da kwamitin tantancewa ya bankaɗo a matsayin ma’aikatan bogi a farkon wannan shekarar.

“Bayan cikkakken bincike da ma’aikatar mu ta yi, mun gano cewa Malaman su 301 da abin ya shafa sunayen su sun shigo cikin Malaman bogi bisa kuskure a cikin malaman bogi guda 780, shi ya sa muka rubuta wa gwamna Dauda Lawal wasiƙa domin a dawo da su bakin aikinsu domin malamai ne na gaskiya”. Yace

Kwamishinan ya yabawa gwamnan bisa yadda yake sauraron matsalar alummar sa, inda ya bada tabbacin cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da ingantaccen ilimi ga ɗaukacin yaran jihar.

“Za mu jajirce wajen ganin cewa ƙwararrun malamai ne kaɗai suke cikin harkar koyo da koyarwa a jihar da nufin samun ingantaccen ilimi a tsakanin yaran mu”. Yace

Kwamishinan ya yi kira ga malaman da aka dawo da su da su ƙara himma a makarantun su, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci sakaci a bakin aiki ba.

“Muna kira ga ɗaukacin malamai 303 da aka dawo da su aiki da kuma waɗanda ke bakin aiki da su bi tsare-tsare na gwamnati tare da jajircewar su wajen yi wa jihar hidima domin samar wa jihar alumma ta gari a nan gaba”. Watatau Madawaki yace

By ukarofi