Yadda afuwar da Tinubu ya yi wa wasu masu harƙallar miyagun ƙwayoyi ta bar baya da ƙura

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Matakin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka na yin afuwa ga mutane kusan 50 da aka yanke wa hukunci sakamakon laifuka na miyagun ƙwayoyi ya bar baya da ƙura a yayin da wasu ke gargaɗin cewa matakin na aika wani saƙo marar fasali game da yakin da Nijeriya ke yi da miyagun ƙwayoyi.

Mutane 50 ɗin na cikin jumullar fursunoni 175 da suka rabauta da afuwar da majalisar bai wa shugaban ƙasa shawara a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Mafi yawan waɗanda aka yafewa cikin 50 ɗin nan an same su da laifin ko dai safarar miyagun ƙwayoyi kamar hodar iblis da tabar wiwi da tiramadol.

A cewar fadar shugaban ƙasa, wannan afuwa ta biyo bayan shawarar da kwamitin bai wa shugaban ƙasa shawara suka yi, suna masu buga misali da waɗanda suka yi nadama da nuna kyakkyawan hali da ma koyon sana’o’i.

Wasu dai an yafe musu bakiɗaya a yayin da wasu da suka haɗa da masu garkuwa da mutane da masu kisan kai suka samu rangamen yawan shekarun da za su shafe a gidan yari. Jerin sunayen ya ƙunshi waɗanda “aka samu da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da ma’aikatan gwamnati da masu safarar ƙwaya da suka yi nadama da ‘yan ƙasar waje… ” inji mai magana da yawun Shugaban ƙasa Bayo Onanuga.

A yayin da yake nuna damuwarsa game da wannan mataki na afuwa, lauya mai rajin kare haƙƙin bi’adama, Inibehe Effiong, ya bayyana matakin da cewa zai ƙarfafa wa masu aikata laifi guiwa da raunta tsarin adalci a ƙasar nan.

Effiong ya bayyana wa Blueprint Manhaja cewa matakin shugaban ƙasa ya ɗauka ya tada batutuwa na duba ɗa’a da kuma shari’a na irin saƙon da ake aike wa da ‘yan Nijeriya da jami’an tsaro.

“A ra’ayina, yafe musu da shugaban ƙasa ya yi zai ƙarfafa ayyukan ta’addanci ne a ƙasar nan,” ya faɗa.

Sannan ya ce sashe na 175 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ne ya bayyana shugaban ƙasa “iko marar shinge kan iya aiwatar da afuwa wanda ya shafi yafiya ga waɗanda aka yanke wa hukunci ko suke fuskantar tuhuma.”

“Abin da hakan ke nufi shi ne afuwar za ta goge duk wani tarihi na aikata laifi.

Lauyan ya yi tambaya game da dalilin bai wa mutane da aka yanke wa hukunci afuwa.

“Ina ƙokarin fahimtar dalilin da ya sa shugaban ƙasa da kwamitin za su yafe wa waɗanda ba su cancanta ba.”

A cikin jawabin da ta fitar a ranar Litinin, Amnesty International, ta nuna damuwarta game da matakin da Tinubu ya ɗauka na yin afuwa ga mutanen da aka samu da laifin take haƙƙin bil’adama.

ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasa ya sake duba matakin da ya ɗauka na yin yafiya ga wasu mutane da suka aikata laifin take haƙƙin bil’adama da kuma tabbatar da haƙƙin waɗanda aka take wa haƙƙinsu da iyayensu.

“Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka zai jawo naƙasau ga al’amuran shari’a tare da murƙushe gaskiya da yanke hukunci a kotuna tsakanin masu gaskiya da marasa gaskiya da kuma yin watsi da kare haƙƙin bil’adama.

A yayin da NDLEA ke aiki “ba tare da tsoro ko nuna son kai ba”, masu fashin baƙi na ganin cewa yafewa waɗanda aka yanke wa hukunci saboda laifuka na ƙwayoyi zai ƙara ƙarfafa harkar safarar miyagun ƙwayoyi ne kawai.

Wasu daga masu laifukan safarar ƙwayoyi da aka yi wa afuwa: Aluagwu Lawrence, 47, an yanke masa hukunci a shekarar 2015 saboda sayar da hodar iblis.

Ben Friday, 60, an yanke masa zaman gidan kaso na shekara uku ko biyan tarar Naira miliyan 1.3 a shekarar 2023 saboda samunsa da tabar wiwi.

Oroke Michael Chibueze, 21, an yanke masa shekara 5 saboda mallakar tabar wiwi a shekarar 2023.

Kelvin Christopher Smith, 42, an yanke masa shekara 4 saboda shigo da hodar iblis a shekarar 2023.

Azubuike Jeremiah Emeka, 31, an yanke masa shekara 5 ko zaɓin biyan tarar Naira miliyan 3 saboda shigo da hodar iblis a shekarar 2021.

Akinwande Adebiyi, 47, an yanke masa hukuncin shekara 3 saboda ta’ammali da tiramadol a shekarar 2023.

Ahmed Adeyemo, 38, wanda aka yanke wa shekara 15 saboda tabar wiwi ya shafe shakara 9 da wata biyar a Kirikiri kafin daga baya a yafe masa.

Adeniyi Jimoh, 31, da Seun Omirinde, 39, dukkansu an yanke musu shekara 15 a shekarar 2015 saboda safarar miyagun ƙwayoyi waɗanda su ma aka yi wa afuwa.

Safiyanu Umar, 56, wanda aka yanke wa hukuncin ba tare da zaɓin tara ba a shekarar 2023 saboda samunsa da kilogiram na 5 cannabis sativa.

Hamza Abubakar, 37, an yanke masa hukuncin zaman kaso na shekara 5 a 2022 saboda sayar da hodar iblis.

Emmanuel Eze, 49, an yanke masa shekara 5 a 2022 saboda hodar iblis.

Bala Azika Yahaya, 70, wanda aka yanke wa shekara 15 a shekarar 2017 saboda sayar da tabar wiwi.

Muharazu Abubakar, 37, wanda aka yanke wa shekara 5 saboda sayar da hodar iblis a shekarar 2022 bayan shafe shekara 3 a jihar Katsina.

Adam Abubakar, 30, da Emmanuel Yusuf, 34, dukkansu an yanke musu hukuncin a shekarar 2022 saboda mallakar kilogiram 2 na Tiramadol.

Jonathan Asuƙuo, 28, yanke masa hukuncin shekara 5 a 2022 sabooda mallakar hodar iblis da sauran ƙwayoyi.

Abiodun Elemero, 43, an yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a shekarar 2014 saboda sayar da hodar iblis bayan shafe shakara 10 a gidan yarin Kirikiri.

Sauran waɗanda aka yi wa sassauci ko aka wanke sun haɗa da: Ifenna Kennechukwu, 42, an yanke masa shekara 20 a 2015 saboda shigo da hodar iblis wanda aka rage wa yawan shekarunsa zuwa 12.

Patrick Mensah, 40, da Obi Edwin Chukwu, 43, wanda aka samu da laifin safarar ƙwayoyi da aka rage masa shekarun zama a gidan yari zuwa shekara 10.

Napolo Osariemen, 61, an yanke masa hukunci a shekarar 2022 saboda samunsa da kilogiram 2 hodar iblis — a yanzu zai yi shekara 7 a maimakon 15.

Helen Solomon, 68, Okoye Tochukwu, 43, da Ugwueze Paul, 38, kowannensu kan laifin da ya shafi tabar wiwi waɗanda aka rage musu yawan shekarunsu zuwa 5.

Chukwudi Destiny, 36, wanda aka yanke hukuncin saboda laifin shigo da hodar iblis a shekarar 2022 wanda aka rage masa daga shekara 6 zuwa 4.

By ukarofi