Gombe ta ƙaddamar da shirin AGILE domin tallafa wa mata

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin tallafin karatun ‘yan mata na AGILE tare da tallafin gyaran makarantu (SIGs), domin inganta ilimi da ƙarfafa ‘yan mata a faɗin jihar.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a otal ɗin Custodian da ke Gombe, inda mataimakin gwamna, Dakta Manasseh Jatau, ya wakilci gwamnan.

Ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma, musamman wajen bai wa ‘yan mata damar ci gaba da karatu da samun ilimin zamani.

“Idan ka ilmantar da ‘ya mace, ka ilmantar da al’umma; idan ka ƙarfafa ta, ka ƙarfafa gaba ɗaya zuri’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Gombe za ta ci gaba da kawar da duk wani cikas da ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, tare da tabbatar da ci gaba da haɗin gwiwa da bankin duniya, ma’aikatar Ilimi ta tarayya, da kwamitin Shirin AGILE domin ɗorewar nasarar shirin.

A nata jawabin, Kwamishiniyar Ilimi, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin gwamnatin Inuwa Yahaya na sauya fasalin ilimi a jihar.

Ta ce kuɗaɗen tallafin za su taimaka wajen gyaran makarantu, inganta yanayin koyo da koyarwa, da kuma ƙarfafa tsarin kula da makarantu ta hannun SBMCs.

Ita ma, kodinetar shirin AGILE, Dokta Amina Haruna Abdul, ta bayyana cewa dubban ‘yan mata a makarantun sakandare za su ci gajiyar tallafin domin rage matsin tattalin arziki da ke hana su ci gaba da karatu.

Ta yaba da jajircewar Gwamna Inuwa Yahaya wajen bai wa fannin ilimi fifiko, tana mai cewa hakan ya ƙarfafa ƙwarin gwiwar ‘yan mata da ya farfado da burin su na neman ilimi a faɗin Jihar Gombe.

By ukarofi