Daga RABIU SANUSI a Kano
Wasu ɗaliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko ɗangote da ke Wudil a Jihar Kano sun karrama Manajan Darakta na KAROTA, Dr. Faisal Mahmud Kabir da shaidar girmawa.
ɗaliban waɗanda sukekKaratun Digiri na Part Time sun yi wannan yunƙurin ne ganin irin hidimar da Manajan Daraktan hukumar ta KAROTA yake wajen tallafawa ilimi a faɗin Jihar Kano.
Da yake ƙarin bayani , Shugaban ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Kwamared Ibrahim Shafir Hashim ya ce wannan ziyara na da nasaba da irin ƙoƙarin Shugaban na KAROTA wajen tallafawa ɗalibai daga makarantu daban-daban.
Kwamared Ibrahim Shafir ya cigaba da cewa MD KAROTA yana kuma ɗaukar nauyin ɗaliban da har su kammala karatunsu a ciki da wajen jihar.
“Abinda ya ba mu sha’awa shi ne yadda Dr Faisal yake tallawa babu wata wariya ko bambanci ta aƙidar siyasa, shi dai buƙatar shi a samu ilimi.”
Shugaban ɗaliban ya ƙara da cewa suma ma’aikatan hukumar ta KAROTA ya basu damar dukkan wanda yake da takardar shedar kammala sakandire kuma yake da buƙatar cigaba da karatu da ya koma zai tallafa masu.
“Wannan kaɗan ne daga cikin irin ƙoƙarin da yake yi kuma ya bamu ƙwarin gwuiwa wajen ziyarar ofishin sa tare da karrama shi.
A nashi jawabin shugaban hukumar ta KAROTA Dr Faisal Mahmud Kabir ya fara da nuna farin cikin shi bisa wannan yunƙuri na ɗaliban.
Manajan Daraktan ya tabbatar da cewa wannan ƙoƙari na ɗaliban yana da matuƙar tasiri musamman karatun part time da yake bakowa yake iya shi ba saboda wasu dalilai na rayuwa.
Dr. Faisal ya buƙaci ɗaliban da su yi tunanin samar da wata kafa da za ta taimakawa waɗanda basu samu damar da za su cigaba da karatu ba suma.
“Wannan karatun da kuke gani kamar gobe ne zaku ga kowa ya kammala shi, saboda shi Karatu indai kana yi tare da maida hankali komin dadewa za ka ga ka gama shi.
Ya ce wannan hukuma a shirye take wajen basu goyon baya da dukkanin hadin kan da suke bukata don cimma nasarar abinda suka sanya a gaba.
“Ku yi ƙoƙari wajen ƙarfafawa matasa, ‘yan kasuwa da ma’aikata gwuiwa wajen ganin su ma sun shigo wannan tsari na karatun part time da sauran karatuttuka.
Haka zalika ya ce dukkan ma’aikatan KAROTA da suke part time za su yi wani tsari da zai taimaka masu wajen samun irin wannan damar.
Ya ce kamar yadda aka dani buƙatar gwamnatin Jihar Kano a yanzu shine samar da Ilimi ga dukkan al’ummar ta, kuma shine matakin farko da Maigirma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya gaba.
Kuma idan al’umma suka samu ingantaccen ilimi kuma sahibi shi ne za ka ga jama’a na rayuwa kan tafarki mai kyau.
