Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban kasuwannin Sabon Gari, Singa da Galadima, Alhaji Abdul Bashir ya raba wa mata kimanin ɗari da hamsin jarin dubu goma-goma ga kowaccensu.
A jawabin shi, Manajan Daraktan kasuwannin Sabon Gari, Galadima Alhaji Abdul Bashir ya ce yana ƙara godiya ga Allah bisa wannan nasarar ta yau da ya yi namijin ƙoƙarin.
Shugaban rukunin kasuwannin ya ce wannan tunani na yau na da nasaba da irin ƙoƙarin mata bisa riƙe amana da jajircewa da suke da shi a dukkan rayuwar.
Yace wannan karon sun ɗauko mata 150 don basu wani ɗan tallafi wanda ba shi da yawa don suma su cigaba da sana’a ko da ƙarama ce dan dogaro da kai tare da taimakon iyalansu.
Abdul Bashir ya kuma bayyana batun Katin Zabe wanda a yanzu shine mai matuƙar tasiri ga dukkan ɗan Jam’iyyar NNPP don cigaba da samar da shugabanci nagari a faɗin Jihar Kano.
“Wannan ne tsarin Kwankwasiyya da muke ciki ƙarƙashin jagorancin Engr. Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya ɗora mu kan shi, tare da Maigirma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf da yake jagorancin Jihar Kano.
“Nan gaba kaɗan za mu ƙara baiwa matasa maza mutum ɗari uku irin wannan jarin don su ma suna gwagwarmaya cikin wannan tafiya mai albarka ta NNPP, bayan nan kuma za mu ƙara bai wa wasu matan da ba su samu ba.
Abdul Bashir ya kuma ƙarin haɗin kan dukkan al’ummar ƙaramar hukumar Gwale don cigaba da samun tagomashi wanda zai ƙara ba wannan gwamnati damar yin nasarar a zaɓe mai zuwa.
A nashi ɓangaren Shugaban ƙaramar Hukumar Gwale Hon Abubakar Mu’azu Mojo ya ce wannan yunƙuri na Manajan Daraktan kasuwannin Sabon Gari da Galadima abu ne mai kyau da kowa ke buƙatar shi.
Mojo ya ce wannan tsari na daya daga cikin tsarin Maigirma Gwamna na bai wa mata da matasa jari, don haka MD ya yi namijin ƙoƙari tare da fatan sauran jagorori za suy i koyi.
“Yanzu a ƙaramar Hukumar Gwale Babu wanda bai san ana wannan taro ba, don haka mu a ƙaramar hukumar mu duk wanda ya samu sai ya bai wa wasu suma su casa.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce irin aikin alkhairin da gwamnan yake yi a faɗin Jihar Kano dole ne a yi masa jinjina, kuma dole mu ƙara zaɓar shi a karo na biyu.
Shi ma a nashi jawabin Manajan Daraktan na hukumar Tourism Tukur ya ce buƙatar shi a nan shine jama’a su fito don cigaba da samun katin zaɓe.
MD yace wannan ya sa a zabe mai zuwa za a samu nasarar komawa a zaɓe mai zuwa tare da samun nasarar Jam’iyyar NNPP a faɗin Jihar Kano.
Suma wasu daga cikin jagororin Jam’iyyar NNPP daga ƙaramar hukumar Dala sun ce wannan na cikin abinda yake mai kyau da Gwamna ya assasa a ciki da wajen Jihar Kano.
A ɓangaren waɗanda suka amfana da wannan tallafi sun yi matuƙar godiya, sannan sun ce za su sanya wannan kuɗi cikin ɗan abin da suke da shi na jari don bunƙasar kasuwanci.
