Daga DAUDA USMAN a Legas
Shugaban ƙungiyar masu sana’ar sayar da dafaffen abinci a Legas, wato masu tuwo, shinkafa da sauran dangoginsu, Alhaji Babangida Mati Musawa, wanda ke gudanar da sana’arsa a kasuwar Mile 12 International Market a Legas, ya shawarci mata Hausawa da sauran ‘yan ƙungiyarsa su ƙara himma wajen tsaftace abincin da suke girkawa don kare lafiyar masu siya da al’umma baki ɗaya.
Alhaji Babangida Mati Musawa, ɗan asalin Jihar Katsina, ya yi wannan jawabi ne a yayin taron wata-wata na ƙungiyar ’Yan Tuwo-Tuwo da aka gudanar a Mile 12, inda suka tattauna kan matsalolin ƙungiyar da hanyoyin magance su, tare da neman dabarun da za su ƙara bunƙasa sana’ar.
A cikin jawabin nasa, Babangida Musawa ya jaddada cewa muhimmancin tsafta a wajen girka abinci ba zai taɓa ƙarewa ba, musamman ganin yadda abinci ke da tasiri kai tsaye ga lafiyar masu siya. Ya ce, “Ya zama wajibi mu kula da tsafta yayin da muke girka abinci da kuma lokacin da muke sayarwa, domin kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da farin cikin kwastomominmu.”
Musawa, wanda ya bayyana kansa a matsayin namiji da ke gudanar da sana’ar mata, ya ce ya shiga wannan sana’a ne domin ƙara wayar da kai ga mata masu sana’ar girka abinci kan muhimmancin bin ƙa’idojin tsafta da kuma yadda za su inganta dandanon abincinsu. Ya ce, “Ni namiji ne, ba mace ba, amma na tsunduma cikin wannan sana’a domin zama abin koyi, da kuma nuna cewa kowane aiki mai halas babu wanda ya ke sama da ɗan uwansa wajen gudanar da shi.”
Haka kuma, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar su ci gaba da bin dokokin kasuwar Mile 12 International Market da goyon bayan shugabanta, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, a kokarinsa na kawo ci gaba da zaman lafiya a kasuwar.
Alhaji Babangida ya kuma jawo hankalin Hausawa mazauna Legas, musamman waɗanda ba su da katin zabe (PVC), da su tashi tsaye wajen sabunta rijistarsu kafin lokacin zabe mai zuwa, domin su sami damar taka rawar gani a zabubbuka.
A ƙarshe, ya yi addu’a ga Nijeriya, yana roƙon Allah ya ba kasar zaman lafiya, cigaba da albarka ga al’umma baki ɗaya.
