Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke cikin gida da wajen ƙasa da su daina ɓatanci da ɓata sunan ƙasar, yana mai cewa lokaci ya yi da za a riƙa tallata ƙasar da nuna kishin ƙasa da fata mai kyau ga makomarta.
Umahi ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja, inda ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ke yaɗa maganganu masu tozarta ƙasar ba tare da hujja ba.
“Ina jin zafi sosai idan na ga mutane suna ɓatanci ga ƙasarsu — a ciki da wajen Nijeriya — suna zagi da suka ba tare da sani ba,” inji shi. “Aiki yakan zama mai sauƙi ne idan kai ba kai ke yin sa ba. Lokaci ya yi mu sake tunani.”
Ya ƙara da cewa, wajibi ne ‘yan ƙasa su riƙa zama masu kishin juna da yin abubuwa da tsoron Allah domin samun alheri mai ɗorewa bayan rayuwa.
“Abin mamaki ne yadda mutanenmu idan sun fita ƙasashen waje suke jure wahala, suna aiki har sa’o’i 19 a rana, suna kuma bin doka da oda. Amma idan sun dawo gida, sai su saba wa doka. Wannan ba daidai ba ne,” inji Umahi. “Wajibi ne mu nuna bege a nan gida. Wannan ita ce ƙasa guda tilo da za ka iya samun ci gaba da gaske a cikinta.”
Ministan ya ce, akwai damar arziki da yawa a Nijeriya, amma mutane ba za su gan su ba muddin suka rufe idanunsu da rashin fata mai kyau.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su riƙa zama masu kyakkyawar fata, su guji fushi da ƙin godiya, yana mai cewa hakan ba zai haifar da ci gaba ba.
“An ce gafara tana ‘yantar da wanda aka daure, kuma idan aka yafe maka, za ka gane kai ne ainihin wanda aka daure. Don haka mu riƙa aiki da tsoron Allah, mu goyi bayan gwamnati, sannan mu yi suka cikin girmamawa. Nijeriya tana komawa ga ɗaukaka,” inji shi.
Umahi ya yaba da jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen fuskantar matsalolin tattalin arzikin da gwamnatin baya ta bari, yana mai cewa ƙin yin korafi da shugaban ya yi a bainar jama’a alama ce ta ƙarfin shugabanci.
“Na san abin da gwamnatin Tinubu ta gada, komai ya zama fifiko, kuma nauyin bashi ya yi tsanani matuƙa. Wasu ma daga cikin bashin ana biyan su ne daga kuɗin da aka ware don manyan ayyuka. Wannan shi ne tushen matsalar,” inji shi.
Ya bayyana cewa yawancin bashin da aka gada ba a yi amfani da su wajen gina abubuwan more rayuwa ba, da hakan zai zama hanyar bunƙasa ƙasa.
“Duk da haka, za mu ci gaba da jajircewa. Har ma man fetur ɗinmu an riga an sayar da wasu kafin lokaci. Amma shugaban ƙasa yana da jarumta, shi ya sa baya korafi. Mun san za mu yi nasara,” inji Umahi.
Ministan ya ƙara da cewa, alamomin tattalin arziki suna nuna cewa gyaran da ake yi yana samun nasara, yana mai cewa hauhawar farashin kaya ya fara sauka, tattalin arziki yana tashi sama da kaso 4.23%, sannan ajiya ta ƙasa wato foreign reserve ta haura fiye da kaso 42%.
“Alamomin suna da kyau, gyare-gyaren gwamnati na aiki yadda ya kamata. Idan muka ci gaba da nuna kishin ƙasa da kyakkyawan fata, ba shakka Nijeriya za ta zama abin alfahari ga kowa,” inji Umahi.
