Iyalan Daddy Lumba sun fitar da sanarwa kan rikicin aurensa da gadonsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Iyalan fitaccen mawaƙin ƙasar Ghana, Daddy Lumba, sun fitar da wata doguwar sanarwa da ta fayyace muhimman abubuwa guda shida da ke cikin rikicin da ake yi kan aurensa, kadarorinsa, da shirin jana’izarsa. Wasiƙar, wadda iyalan Fosu suka sanya hannu a kai, ta bayyana matsaloli da ke ta ƙara hargitsa dangantaka tsakaninsu da budurwarsa, Akosua Serwaa.

Manyan abubuwa shiga da wasiƙa ta ƙunsa su ne;

1. Rashin amincewar Akosua Serwaa da sauya matsuguni

Iyalan sun zargi Akosua Serwaa da ƙin amincewa da buƙatun da marigayi Daddy Lumba ya taɓa yi mata na ta koma tare da shi a wasu lokuta. Wannan, a cewar su, ya janyo sanyin dangantaka tsakaninsu da sauran iyalan.

2. Saɓani kan wurin da za a gudanar da jana’iza

A cewar wasiƙar, Akosua Serwaa ta nuna ƙin amincewa da wasu daga cikin wuraren da aka ba da shawarar a yi jana’izar marigayin. Wannan saɓanin ya janyo jinkiri da rikice-rikice kan inda za a binne fitaccen mawaain.

3. Rikici kan mallakar kadarori

Iyalan Fosu sun bayyana cewa akwai tashin hankali kan wanda ya dace ya kula da kadarorin marigayi, suna zargin Akosua Serwaa da ɗaukar muhimman matakai ba tare da tuntuɓar iyalan ba, wanda ya sa suka ce ta take al’adar gida.

4. Rashin gaskiya da buɗaɗɗen bayani

Iyalan sun nuna damuwa cewa ba a bayyana cikakken bayani kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi jana’iza da kadarorin marigayin. Sun nemi a tabbatar da gaskiya da haɗin kai don a kiyaye adalci da al’ada.

5. Tambaya kan sahihancin aurensu

Wani muhimmin abin da wasiƙar ta bankaɗo shi ne tambayar matsayin auren Daddy Lumba da Akosua Serwaa — ko an tabbatar da shi bisa doka da al’ada. Iyalan sun ce wannan rashin tabbas ya ƙara jefa lamarin cikin rikici, musamman kan gado da shirye-shiryen jana’iza.

6. Kiran bin tsarin gargajiya

A ƙarshe, iyalan Fosu sun roƙi a girmama tsarin al’adar gargajiya wajen yanke duk wata hukunci da ta shafi jana’iza, kadarori, da gado. Sun ce a al’adance, shugabannin iyali da dattawa ne ke da ikon kula da irin wannan lamari bisa tsarin ƙabilar Ashanti.

Rikicin ya samo asali ne daga sabanin dokokin gadon Jamus (inda Daddy Lumba ya taɓa rayuwa) da dokokin gargajiyar Ashanti. Masana shari’a sun ce irin wannan rikici na bayyana yadda tsarin kasashen Turai ke iya sabawa da tsarin gargajiya na Afirka.

A halin yanzu, maganganu na ci gaba a tsakanin ɓangarorin biyu, yayin da masoya mawaƙin da jama’a ke kira da a sasanta lamarin cikin lumana, domin a girmama gadonsa da mutuncin da ya bari a tarihin waƙar highlife ta Ghana.

By ukarofi