Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Nijeriya.

Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ƙa’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki.

Hukumar Hana Fatucin Mutane ta ƙasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harƙallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, waɗanda su ba su je kotun ba a ranar.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu ce ta bayar da umarnin kullewar yayin fara sauraron shari’ar, bayan sauraron buƙatar lauyan masu ƙara, Salisu Muhammad Tahir da na wanda ake ƙarar, Gideon Uzo.

Daga nan ne kuma kotun ta dage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba inda ake sa ran za a gurfanar da Christpher tare da sauran waɗanda ake zargin.

An dai kama Chrispoher ne bayan wani samame da jami’an hukumar ta NAPTIP suka kai gidan nasa da ke jihar Delta sannan suka ceto yara takwas da ake zargin ya sace su daga Kano sannan ya kai su gidan marayun nasa da ke Asaba, babban birnin jihar ta Delta.

By ukarofi