Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na inganta harkar wutar lantarki ta hanyar haɗin guiwa da amfani da sabbin fasahohi.
Dikko ya faɗi haka ne a lokacin da ya halarci taron kwana biyu tare da gwamnonin Kano da Jigawa da jami’an kamfanonin KEDCO da Future Energies Africa a birnin Marrakech na ƙasar Maroko.
Taron ya mayar da hankali kan yadda za’a samar da wuta ga yankunan da ba su da hasken lantarki, inganta tashoshin samar da lantarki, kawar da ƙarancin lantarki, da kafa hukuma ta bai ɗaya da za ta daidaita hanyoyin samar da lantarki a yankunan.
Ya jaddada cewa jihar Katsina na samar da hasken rana da iska, kuma gwamnati za ta yi amfani da shi don farfaɗo da tattalin arziki da samar da wutar lantarki da ta dace ga al’umma da masana’antu.
An kammala taron da yarjejeniyar haɗin gwiwa domin zuba jari a cibiyoyin wuta lantarki, faɗaɗa samar da sabbin makamashi na zamani, da sauran su.
Tawagar gwamnatin jihar Katsina ta ƙunshi Kakakin majalissar dokoki ta jihar Rt.Hon Nasir Yahaya, mai ba gwamnan shawara kan nakamashi da lantarki Dakta Hafiz Ibrahim, babban manajan hukumar samar da lantarki a karkara Injiniya Abubakar Matazu, mai taimaka ma gwamnan akan makamashi na zamani Injiniya Engr Abdulaziz Abdullahi Kabir.
