An ƙaddamar da ƙungiyar Musa Adamu Funtua Network for Gwagware Countinuity 2027

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamred Mannir Suleiman shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua shine sabon shugaban ƙungiyar tare da mutane 11.

Da yake jawabi bayan da ya amshi ragamar shugabancin ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya nuna jin daɗin na yadda ya ga mutane masu mutunci masu ƙima kuma ya ƙara da cewa” fuskokin da ya gani dama “irinsu muke son muyi aikin wannan ƙungiya tare dasu”, a cewar sa.

Manufar wannan ƙungiya, ƙungiya ce wadda za ta bada nata gudunmawa wajen taya Gwamna DIkko Raɗɗa yaƙin neman zaɓe a karo na biyu duba da Irin cikin ɗan lokaci kaɗan ya kawo gagarumin cigaba a yankin Funtua.

Kwamared Suleiman ya bayyana cewa a karon farko a tarihin Funtua,”yau gashi muna da jami’a ga manyan tagwayen hanyoyi da sauran wasu ababen more rayuwa a yankin duk a lokacin mulkin Dikko Raɗɗa.

Shi yasa wannan sabuwar ƙungiya ƙarƙashin uban tafiya Hon Musa Adamu Funtua za ta maida biki.

Sabon shugaban ƙungiyar ya karɓi jagorancin ne daga Alhaji Hassan Damina.

Hon. Muntari Lawal Maska shine mataimakin shugaba sai Alhaji Nura Sule a matsayin shugaban masu ruwa da tsaki.

Ma’ajin ƙungiya, Alhaji Sanusi Babangida Dakare sai Hon Ado Shahara mai binciken kuɗi.

Mahalarta taron sun tofa albarkacin bakin su, daga ƙarshe anyi addu’o’in neman gafara ga wasu daga cikin ma’aikatan gwamnati da aka rasa a garin Funtua tare da addu’o’in Allah ya zaunar yankin lafiya.

By ukarofi