Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tabbatar da naɗin Hon Yusuf Suleiman Jibiya da Hajiya Aisha Aminu a matsayin Kwamishinoni a majalisar zartarwa ta Jihar Katsina, bayan da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, ya gabatar da sunayensu domin tantancewa da amincewa.
An tabbatar da naɗin ne bayan zaman tantancewa da aka gudanar a zauren majalisa, inda ’yan majalisar suka yaba da gogewar su, ƙwarewa, da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Hon. Yusuf Suleiman Jibia gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma kwararren jami’i wanda ya riƙe muhimman muƙamai da dama a gwamnatin jihar Katsina, ciki har da Kwamishinan Ruwa, Kwamishinan Bayani, Al’adu da Harkokin Cikin Gida, da Kwamishinan Lafiya.
Haka kuma ya taɓa zama daraktan hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Katsina, da babban manajan hukumar motocin Jihar Katsina (KTSTA).
Ɗan asalin ƙaramar hukumar Jibiya ne, kuma yana da digiri na farko a fannin Chemistry daga Jami’ar Bayero Kano (BUK). Ya kuma taɓa zama Shugaban ƙaramar hukumar Jibiya har sau biyu, inda ya shahara wajen jagoranci da gudanar da manyan shirye-shirye na cigaba.
Ita ma Hajiya Aisha Aminu, wacce aka tabbatar da ita a matsayin kwamishiniya, gogaggen ’yar kasuwa ce kuma mai ƙwarewa a fannin gudanar da harkokin gwamnati da na kamfanoni. ’Yan majalisa sun bayyana jin daɗin su da irin hangen nesa da ƙwarewar da take da ita wajen jagoranci da samar da cigaba.
Hajiya Aisha a halin yanzu ita ce Daraktar Janar ta hukumar bunƙasa harkokin kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA). Tana da digiri na biyu (MBA) daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) da kuma digiri na farko (B.Sc.) a fannin gudanar da kasuwanci daga jami’ar Abuja.
Tana da dogon tarihin aiki a ɓangaren gwamnati da na masu zaman kansu, musamman a fannin gudanarwa, ci gaban kasuwanci da habakar ma’aikata.
Da yake jawabi bayan tabbatar da su, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Daura, ya taya su murna bisa samun wannan matsayi, yana mai cewa naɗin nasu na nuna ƙudirin Gwamna Raɗɗa na gina gwamnati mai cike da ƙwarewa, ƙirƙira da haɗa kan kowa.
