MOPPAN ta yaba wa Abdul Amart bisa kai Jaruma Halisa umrah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta yaba wa sanannen furodusa a masana’antar Kannywood, Abdul Amart kan daukar nauyin jaruma Halisa Mohammed zuwa aikin umara.

Sakataren MOPPAN, Dakta Mohd I. Gumel a wata takarda, ya miƙa godiya da jinjina ga furodusan a madadin mambobin ƙungiyar, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tausayi da kulawa ga abokan aiki da ma al’umma baki ɗaya.

Ya ce, “wannan taimakon nasa ba shine na farko ba”, abu ne da ya saba yi wa kowane ɗan masana’antar da ke cikin halin buƙatar a tallafa masa.

Sakatare ya ƙara da cewa, “Hakan yasa muke alfahari da kai kuma muke tinƙaho da dukiyar da Allah ya baka. Allah ya saka maka da alkhairansa.”

“A karshe, ina maka fatan cin gajiyar wani hadisin Manzon Allah (SAW) da na ji malamai suna hakaitowa cewa, ‘Duk wanda ya zama sanadiyar yaye baƙin cikin bawa a nan duniya, to Allah zai yaye masa bakin ciki ranar tashin kiyama’. Allah ya faranta maka kamar yadda ka farantawa Halisa, kuma mu ma ka faranta mana”, inji Sakataren.

By Babaji