
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta dakatar da yajin aikin sati biyu da ta shiga na gargaɗi a dukkanin jami’o’in ƙasar.
ASUU ta sanar da haka ne a yau Laraba, yayin taron ganawa da manema labarai a hedikwatarta da ke Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana haka ga ƴan jarida, inda ya ce hakan ya samu ne a sakamakon shiga tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawa tare da wasu manyan ƙasa suka yi.
Farfesan ya ƙara da cewa, majalisar zartarwar ƙungiyar ta cimma matsayar bai wa gwamnatin tarayyar wa’adin wata guda domin ta warware buƙatunta da aka yi yarjejeniya akansa tsawon lokaci.
