Abuja: Lauyan Nnamdi Kanu ya yanki jiki ya faɗi a kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bayan kwana ɗaya da Alƙali Abubakar Umar Sa’id ya ƙi sanya hannu a takardar belinsa, Lauyan Nnamdi Kanu na musamman, wato Aloy Ejimkor, ya yanki jiki ya faɗi a Kurkukun Kuje da ke Birnin Tarayya Abuja.

A wani rahoto da Lauyan Ejimkor, Maxwell Opara ya fitar, ya ce ya je wata ziyarar aiki amma bai samu ganin sa ba, sannan majiyoyi sun ce ta yiwu an garzaya da shi asibiti ne a sakamakon faɗuwar.

A ranar Litinin aka kama Ejimkor tare da wasu mutane 12 ciki har da ɗan’uwan Kanu, Frins Emmanuel Kanu saboda shiga zanga-zangar neman sakin jagoran na ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB).

A yayin kama su ne aka fesa musu barkonon tsohuwa da lakaɗa musu duka kana aka tafi da su ofishin ƴan sanda.

A halin yanzu Ejimkor na karɓar magani a asibitin kurkukun Kujen duba da yadda halin rashin lafiyarsa ke tsananta.

A kwanan baya ne tawagar lauyoyin da ke kare Kanu a kotu suka janye daga shari’arsa, lamarin da shi da kansa ya tabbatar nan take.

Ana tuhumar jagoran fafutukar ne da laifin ta’addanci da suka shafi ayyukansa na taware, inda aka kama shi a shekarar 2015.

Daga bisani a 2017 aka sake shi, inda a lokacin ne ya fice daga Nijeriya, sannan kuma aka sake kama shi a 2021, wanda tun lokacin yake hannun hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS.

By Babaji