
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Wakilai ta yi ikirarin samun barazana daga ƴan ta’adda cewa za su tarwatsa Majalisar Dokoki a Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban Kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilan, Garba Muhammad ya sanar da haka a yayi taron ji ta bakin al’umma da aka yi a jiya Talata a Abuja.
An shirya taron ne domin nazari akan ƙudirin samar da sashin tsaro a majalisar, wanda ya zayyano cancanta da sharuɗɗan hidima na jami’in tabbatar da doka da oda da tsaro, wato ‘sergeant-at-arms’.
Garba Muhammad ya bayyana cewa majalisar tana fuskantar ƙalubalen tsaro musamman ganin yadda take tara ɗimbin mutane da suka haɗa da ƴan majalisu, ma’aikata, jagorori, masana shari’a, masu zanga-zanga da jami’an tsaro da ke zirga-zirga a kullum a wajen.
Ya bayyana cewa, wannan dalili yasa ƴan ta’adda suke neman damar ta da zaune-tsaye a yankin domin zartar da munanan ayyukansu.
“Mun samu barazana daga ƴan ta’adda cewa za su tarwatsa Majalisar Dokoki da barazana daga masu zanga-zanga na mu rufe majalisar”, inji shi.
Ya ƙara da cewa, ƴan majalisa na samun barazana daga mazaɓunsu da wasu da ke zuwa ba tare da ƙulla alƙawarin haɗuwa ba, lamarin da yasa akwai buƙatar tsaurara tsaro, yana mai kira ga majalisun dokoki na jihohi da su aiwatar da irin salon tsaron.
