Ilimi da gaskiya ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma – Sarki Sunusi II

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa, yin gaskiya da amana shi ne ginshiƙin na cigaban kowace al’umma.

Sarki Sunusi II ya bayyana haka ne a taron ƙaddamar da littafin (All Hands on Deck) na Ms. Arunma Oteh, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja, a ranar Talata.

Littafin All Hands on Deck wacce tsohuwar babbar darakta a bankin duniya Ms. Oteh ta rubuta, ya maida hankali ne kan hanyoyin bunƙasa shugabanci mai nagarta, da gaskiya da amana a harkokin tattalin arziki da mulki.

Sarkin na Kano, ya yaba da wannan aiki na ilimi, yana mai cewa irin waɗannan littattafai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina shugabanni masu hangen nesa da adalci a Najeriya.

Taron ƙaddamar da littafin dai ya samu halartar fitattun shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti; ministan kuɗi, Mista Wale Edun; ministan kasafin kuɗi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu; da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi.

Kazalika cikin mahalartan, akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Pius Anyim da sauransu.

By ukarofi