Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa wani kwamiti da zai duba yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla tsakanin ɓarayin daji da al’ummomin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a faɗin jihar.
An kafa kwamitin ne ƙarkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya jagoranci taron kafa kwamitin tare da ƙaddamar da ayyukansa.
Kwamitin, wanda Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Katsina zai jagoranta, ya ƙunshi wakilai daga hukumomin tsaro da sassan gwamnati. Ciki har da Kwamishinan
harkokin cikin gida da tsaro wanda zai kasance sakataren kwamitin, da kuma wakilai daga rundunar Sojoji ta 17 Brigade, da 213 Forward Operation Base (FOB), da hukumar ‘yan sanda farin kaya, da wakilci daga babbar kotun jihar.
Manufar kafa kwamitin ita ce duba yadda aka gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya, da kuma bayar da shawarwari ga gwamnati kan matakan da za su tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar da kuma tabbatar da cikakken zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
A yayin ƙaddamar da kwamitin, sakataren gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin dabarun Gwamna Raɗɗa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Ya ce, “Gwamnatin Katsina ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an samu zaman lafiya mai ɗorewa a dukkan yankuna. Wannan kwamiti zai bayar da cikakken rahoto cikin makonni biyu masu zuwa domin samar da sahihan matakai na ci gaba.”
Kwamitin zai fara aikin sa nan take, tare da ziyarar sassan da suka fi fuskantar matsalar tsaro domin tattara bayanai kai tsaye daga al’ummomin da abin ya shafa.
Tun fara zaman sulhu tsakanin ‘yan bindiga da alummomin wasu ƙananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro mutane da yawa sun nuna jindaɗin su yadda zaman lafiya ya samu.
To sai wasu na nuna fargaba ga yadda aka gudanar da sulhu a waɗannan yankuna ba tare da ‘yan bindiga sun ajiye makaman su ba.
