Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban fadar ƙaramar hukumar Bichi, Sani Ahmad Bello wanda ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi R/Lemo, ya ce, ƙaramar hukumar Bichi ta ɗauki nauyin ɗaliban tun daga matakin farawa zuwa gama karatun; kama daga kuɗin makaranta, unifom gami da abinci, a makarantun Kazaure, (Collage Of Nursing) da (Dambo College Of Health Science And Innovation Kazaure), inda wasu za su ɗauki tsawon shekaru uku wasu kuma shekaru huɗu kafin su kammala.
Sani Ahmad ya ci gaba da cewa, ɗaliban sun rabauta da wannan tagomashi ne sakamakon bita da jarabawa da ƙaramar hukumar Bichi ta yi musu, domin a tantance su tare da tabbatar da cancantarsu bisa sharuɗa na abubuwan da makarantun suke buƙata ga kowane daliblɓi, a wannan bigire na karatun lafiya.
“Waɗanda za su yi (other health courses) ɗin su ma; Medicine, Laboratory Science, Pharmacy, da Community Health (CHEW) an biya musu duka kuɗinsu, kawai abin da ya rage wa yaro ya haɗa kayansa ranar da za a kai su, kuma daɗin-daɗawa ma hatta kuɗin motar da za ta kai su ducumentation ƙaramar hukuma ta biya musu.” In ji shi.
Kazalika ya ce, nan gaba karamar hukumar za ta sake ɗaukar nauyin karatun wasu ɗaliban kimanin mutum talatin (30) domin cigaba da gina harkokin matasa tare da bunƙasa iliminsu. Bisa haka jami’ar yaɗa labaran ta tuntuɓi waɗannan ɗalibai da suka amfana a matakin farko, jim kaɗan bayan ganawarsu da shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata yayin gabatar masa da su.
“Asali dama burina na taimaki jama’a, wannan karatu idan Allah ya ba da sa”a aka yi zai sa na cim ma burina na taimakon al’uma.” Ɗalibi Sa’adi Ibrahim Muhammad Jar Kasa.
“Kuma za mu dage mu yi abin da yakamata domin mu fitar da shugaban ƙaramar hukuma kunya, sannan kamar yadda ake samun matsaloli a asibitoci; ka je wani lokacin ba likita ko a ki sauraren mutane da wuri, in sha Allahu ta ɓangare na ba za a samu wannan matsalar ba.” Ɗaliba Rukayya Tasi’u Ado mazaɓar Bichi.
A jawabin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya yi godiya ga Allah tare da jinjina wa gwamnatin jiha, bisa ɗaukar nauyin karatun ɗalibai da take yi a ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar nan, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf a kowane fanni, musamman ɓangaren lafiya uwar jiki, inda a ƙarshe ya ja hankalin ɗaliban da suka rabauta a wannan fanni dake ƙaramar hukumar Bichi.
“Muna ba su shawara da su je su zage dantse! Kada su bar gida da niyyar sun tafi karatu kuma su zama wani abu daban; wannan shi ne dalilin da ya sa muka tara su muka ja hankalinsu, a kan lallai su je su zama wakilai na gari ga ƙaramar hukuma da jiha da ma ƙasa baki ɗaya.” In ji shi.
