Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaryata ikirarin da Cibiyar Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism (WSCIJ) ta yi cewa jihar tana cikin jerin jihohin Najeriya da ke fiye da kowa take ’yancin kafafen yaɗa labarai.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana rahoton a matsayin mai cike da ruɗani kuma ba shi da tushe daga gaskiyar da ke faruwa a jihar.
Comrade Waiya ya nuna godiya ga kafafen yaɗa labarai bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban siyasa, zamantakewa da tattalin arzikin Kano, tare da jaddada ƙudirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ci gaba da goyon bayan aikin jarida na gaskiya, gaskiya a mulki, da ƙarfafa hulɗar gwamnati da jama’a.
“Wannan rahoton da Cibiyar Wole Soyinka ta fitar mai taken ‘Shrinking Freedoms 2024’ bai nuna ainihin halin da kafafen yaɗa labarai ke ciki a Kano ba. Wannan tunanin ne kawai na wasu masu zaune a ofis suna kiran kansu ’yan jaridar bincike.
Kwamishinan ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf mutum ne mai son kafafen yaɗa labarai, inda ya ce an yaba masa sau da dama daga manyan kafafen labarai bisa gaskiya da buɗe kai wajen gudanar da mulki.
“Gwamna Yusuf ya samu lambar yabo daga aƙalla ƙungiyoyi biyar na kafafen yaɗa labarai, ciki har da Blueprint, Leadership, da Nigerian NewsDirect, saboda gaskiyarsa, jarumtar jagoranci, da gudunmawarsa ga ilimi da kiwon lafiya.”
Ya kuma lissafo wasu muhimman ayyuka da ke nuna kyakkyawar dangantakar gwamnati da kafafen yaɗa labarai, irin su:
Karɓar taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ).
Goyon bayan kafa NUJ Online Chapel.
Da shirya tarukan tattaunawa a duk bayan wata uku tsakanin gwamnati da shugabannin kafafen yaɗa labarai domin nazari da musayar ra’ayoyi.
Waiya ya ƙara da cewa Jihar Kano na ci gaba da tallafawa cigaban jaridar zamani da fasahar watsa shirye-shirye, inda ya bayyana cewa:
“Muna a matakin ƙarshe na shirya taron ƙasa na ƙungiyar ’ƴan watsa labarai ta Najeriya (Nigerian Society of Broadcasters) domin ƙarfafa ƙa’idojin sana’a da ɗabi’a a aikin jarida.”
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Yusuf na ci gaba da huldar gwamnati da jama’a ta hanyar tattaunawa da ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) da kuma kula da zanga-zangar lumana.
“Gwamna Yusuf kansa ne ya karɓi masu zanga-zanga a fadar gwamnati, ya saurari ƙorafinsu, sannan ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa tana kan aƙidar gaskiya da mulkin jama’a,” in ji shi.
A ƙarshe, Waiya ya buƙaci cibiyar Wole Soyinka da makamantansu su tabbatar da yin bincike na ainihi kafin su fitar da rahotannin da ka iya kawo ruɗani ko yaudara ga jama’a.“Irin waɗannan rahotanni na ƙarya ba kawai suna ɓata sunan jihohi irin Kano ba ne, har ma suna rage ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da ’yancin jarida, gaskiya a mulki, da haɗin kai tsakanin gwamnati da jama’a.
