Makarantar Tanwirul Azhar ta yi taron saukar Alƙur’ani da mauludin Annabi

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanar da taron saukar karatun Alƙur’ani Karo na biyar na makarantar Tanwilur Azhar li tahafizil ƙur’an a ranar Lahadi.

Taron ya samu halartar iyayen ɗalibai maza da mata da iyayen ƙasa da manyan gwanayen Alƙur’ani.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a taron saukar wanda ya assasa makarantar Malam Muhammadul Hadi da ake wa laƙabi da Malam Bala, ya ce an assasa makarantar ne kusan shekaru 13 kenan da manufar sunan ta na “kore duk wani abu na rashin sani a ƙwaƙwalwa a cusa masa Alƙur’ani da tarbiyya” sun fara ne  da ɗalibai  daga  runfarsa na gida da ɗalibai ‘ya’yansa su biyar da malamai biyu amma karatun da suke yi ya janyo makarantar sai da ta zama tana da ɗalibai 32 a cikin gidansa, daga nan ya sama mata wajen zama ta rushe gidansa ya mayar da muhallin makarantar na dindindin yanzu kuma tanada ɗalibai sama da 500 da malamai 42.

Ya yi nuni da cewa dama can iyaye da kakanninsu na karantar da Alƙur’ani a allo a tsarin tsangaya har yanzu suna nan kan tsangayar mahaifinsa, sai suka ga cancantar faɗaɗa karatun ya tafi da zamani yanda ake buƙata.

Ya ce babban nasara da kafa makarantar ta samu shine kore rashin tarbiyya, a duk inda reshen makarantar take  da tabbatar da tarbiyya don haka ma za ka samu yaron da mahaifinsa suka  gaza ko wani dalili yasa sun ɗauke shi daga makarantar  amma yana da shauƙin zuwa makarantar, ko da ba a turo su ba, suna cuɗeɗeniya da ɗaliban makarantar saboda sha’awarsu da tarbiyya da kyakkyawan mu’amala da ake da shi.

Malam Bala ya ce  tunda suna da tsangaya ta Allo sun fahimci ƙalubale daban-daban da suka saba da su, amma da suka shigo wannan tsari  sai suka ga  sauƙin ƙalubalen, saboda a nan kowane Uba  sai ya yiwa ɗansa rijista ya yarda da manufa da tsarukan makaranta, kuma ɗaliban da suke gaban malami gaba ɗaya ba su wuce 30,40 ba, amma a tsangaya kai ne jagoran mutane ɗaruruwa saboda haka sai suke ganin sauƙin lamarin.

Ya yaba da irin gudunmawa da iyaye da maƙota ke ba su kuma koyaushe suna ba su haƙuri akan duk abinda zai je ya zo domin zama da ‘yan wani sai haƙuri ko naka nema haƙuri kake da shi, suna yi musu juriya kuma suna neman shawarwari daga gare su kowane yanayi ana fahimtar juna.

Malam Muhammadul Hadi ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu da hukumomi duk wata ƙa’ida na hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Gwale a kanta suke tafiya sau da ƙafa suna ba su haɗin kai kuma sun samu tallafi na malamai daga gwamnati ana bai wa malamai da makarantar ta ɗauka horo na sanin makama. 

Malam Balarabe ya yaba da irin gudunmawa da malaman makarantar ke bayarwa, tare da jan hankalinsu da cewa su ƙara duba rayuwar al’umma a wannan lokacin da ake ciki duk wanda ya yiwa ɗan wani gudummawa na alkhari Allah zai yi wa nasa ko yana raye ko baya nan kuma su iyaye su zama masu  haƙuri da hangen nesa in ka bar ɗanka bai tafi makaranta ba a cikin wace ɗabi’a zai kasance su waye zasu zama  abokansa don haka su ɗora su kan neman ilimi.

Saukar karatun dai na wannan karon na ɗalibai guda 65 ne daga ciki maza 33 da kuma ɗalibai Mata guda 32. An raba takardu na shaidar yabo ga malamai da wasu daga cikin al’umma da suke bayar da gudummawa ga cigaban ilimi da tarbiyya. Bayan kammala bikin saukar makarantar ta ɗora da gudanar da maulidin Annabi da ta shirya.

By ukarofi