Cocin ERCC Graceland sun gudanar da taron ranar al’adun gargajiya na 2025

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

Cocin Evangelical Reformed Church of Christ da a ka fi sani da ERCC Graceland dake Lafiya a jihar Nasarawa ya gudanar da wani babban taron ranar baje-kolin al’adun gargajiya ga mambobin cocin na jiha da ƙasa baki ɗaya.

Taron wadda aka gudanar a cikin cocin ya samu halartar mambobin masu yare da al’adu dabandaban a jihar dama saura jihohin ƙasar nan daban daban.

Da yake ganawa da wakilin mu a jihar John D. Wada bayan an kammala taron, babban Rabaran da ke kula da cocin wato Rabaran Moses A. Kudu JP ya bayyana muhimmancin ranar al’adun gargajiyar wadda yace cocin ke gudanar a kowanne shekara da nufin haɗa kawunan duka mambobin daga al’adu daban daban don tabbatar da ƙauna, zumunci da kuma zaman lafiya a tsakanin su.

Yace tabbas wannan ire-iren taron na musamman yana haifar da ɗa mai ido bayan baje-kolin kayayyaki da abinci da tufafi da sauran al’adun gargajiyar mambobin daban daban, hakan yana kuma sanar da damar yin murna tare cikin soyayya da armashi.

Babban Rabaran cocin ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga gwamnatoci a duka matakai musamman a jihar Nasarawar su cigaba da bada fifiko wa shirye-shirye da ayuka dake inganta harkokin al’adun gargajiyar jihar baki ɗaya don a cewar sa idan a na yin haka za a iya rage, ko kawo ƙarshen matsalar rigingimu da yaƙe-yaƙen ƙabilanci da ke aukuwa a kai a kai a jihar. Sannan ya buƙaci mahalarta taron ba kawai su baje kolin al’adun gargajiyar nasu ba amma su tabbatar sun aiwatar da duka abubuwa da suka gabatar a lokacin taron idan suka koma gida don cimma burin ranar.

Tun farko da yake wa’azi game da ranar baje-kolin al’adun gargajiyar, Very Rabaran Dakta Anthony Habila ya ja hankulan mambobin cocin ne da ma al’ummar jihar baki ɗaya su guji yin watsi da al’adun su musamman kalmomin yarukansu da a cewar sa suna da matuƙar mahimmanci a rayuwa.

Ya bayyana takaicin sa dangane da yadda wasu ke ƙin yin yaren su maimakon haka sai su riƙa yin yarukan nasara da hakan yace ko kaɗan bai dace da tarbiyar da a kasan ɗan Afirka ba. Ya kara da cewa Allah baya farin ciki da ire-iren mutanen ba don shi (Allah) ne ya basu baiwar kuma yasan abinda yasa ya basu. Inji shi.

Wakilin namu dai ya rubuto cewar a yayin gagarumin taron ranar baje-kolin al’adun gargajiyar mambobin cocin ERCC Graceland ɗin na bana, an gudanar da wasannin kwaikoyo na musamman irin na al-adu da rera waƙoƙin al’adu da rawa da uwa uba baje-kolin kayayyakin al-adun gargajiyar daban daban daga yarukan da suka hada dana Bagyi da Eggon da Alago da Nungu da Mada da Migili da yaren jihar Filato da na Ribas da sauran su da dama daga ciki da wajen jihar.

By ukarofi