2027: Jam’iyyar APC ta Zamfara ta amince da Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

An amince da wannan zaɓen ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan Sanata Abdulaziz Yari a yau Asabar.

An yanke wannan shawara ne bayan wani ƙudiri da
Sanata Sahabi Ya’u mai wakiltar yankin Zamfara ta Arewa ya gabatar, kuma ɗan majalisar wakilai na tarayya Hon. Abdul Malik Zubairu mai wakiltar Maru da Bungudu ya goyi bayansa a lokacin taron.

Da yake jawabi, Sanata Abdulaziz Yari ya yaba da shawarar da dukkan ‘yan jam’iyyar APC suka yanke na amincewa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo a shekarar 2027.

“Za mu ci gaba da jajircewa kuma mu tsaya tsayin daka kan shawararmu ta amincewa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin babbar jam’iyyarmu ta APC a babban zaɓen 2027 da ke tafe a jihar Zamfara” in ji Yari.

Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC a jihar da su ci gaba da haɗin kai don samun nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da APC a jihar.

A cewarsa, jam’iyyar ba za ta iya yin nasara a zaɓen 2027 mai zuwa ba in har aka kasa samun daidaito, haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba tsakanin ‘yan jam’iyyar a jihar.

“Ba za mu iya cimma nasara ba musamman a zaɓen 2027 mai zuwa idan har muka kasa haɗa kai, don haka akwai buƙatar dukkanin mu mu kasance masu haɗin kai da kuma ci gaba da zama ‘yan ƙasa masu bin doka da oda.” Yaro ya ce

Haka zalika, da yake magana, tsohon gwamnan jihar kuma ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Mohamed Matawalle ya yi kira da a girmama dukkan shugabannin jam’iyyar a jihar.

A cewarsa, siyasa da cin amana, rarrabuwar Kai, munafunci sune abubuwan da ke haifar da gazawar kowace jam’iyya ta siyasa.

Ya ƙara da cewa, waɗanda ke haifar da rarrabuwar kawuna ko kuma yiwa jam’iyyar zagon ƙasa a tsakanin masu ikirarin su halastattun ‘ya’yan jam’iyyar ne a jihar, za a ɗauki ƙwaƙkwaran mataki a kan su.

Matawalle ya tabbatar da cewa APC za ta dawo da martabarta da ta rasa a jihar Zamfara a shekarar 2027.

“Za mu yi aiki tuƙuru don tabbatar da cewa APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyya ɗaya domin nasararta a zaɓen 2027 mai zuwa a jihar Zamfara”. Matawalle ya tabbatar da cewa

Ya buƙaci ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da haɗin kai da kuma zama jakadu nagari don ci gaban APC a jihar Zamfara.

A cikin jawabin sa na fatan alheri, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Tukur Danfulani, ya gode wa dukkan ‘yan jam’iyyar bisa matakan da suka ɗauka bisa tabbatar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zamo a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027 mai zuwa a jihar.

By ukarofi