
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin ƙasar Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya bisa dalilai na tsaro, inda ta nuna damuwarta akan jita-jitar bazuwar dakarun tsaron Amurka a yankin Yammacin Afirka.
Majiyoyin sojoji a N’Djamena yau Litinin, sun tabbatar da Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya umarci sojoji da su rufe dukkan iyakokin da suka raba tsakanin Chadi da Nijeriya.
Hakan na zuwa ne sakamakon wani bayani na sirri da ke nuna cewa ƴan ta’adda da ke ayyukansu a Arewacin Nijeriya na shirin tsallakawa zuwa cikin ƙasar Chadi.
A cewar Zagazola Makama, tuni aka baza dakarun tsaron Chadi da tankokin yaƙi zuwa hanyoyin da ke kai mutane cikin ƙasar daga Nijeriya.
Shugaba Déby ya ci alwashi tare da gargaɗim cewa babu wata ƙungiyar ta’addanci ko dakarun tsaron wata ƙasa da za a bari ta shiga Chadi ta kowane irin yanayi.
Matakin na zuwa ne yayin da ake fargaba da jita-jitar zargin ayyukan sojojin Amurka a yankin Sahel da Afirka ta Yamma.
