Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 31 wajen gina madatsar ruwa ta Zobe

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da ci gaba da aikin madatsar ruwa ta Zobe a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

Aikin wanda aka fara shi tun fiye da shekara 30 da suka gabata, za a kashe kuɗi naira biliyan 31 wajen kammala shi, kamar yadda hukumomi suka tabbatar, inda ake sa ran zai samar da ruwa mai tsafta ga ƙananan hukumomi bakwai ciki, har da Katsina babban birnin jihar.

Gwamnan Katsina Dikko Umaru Raɗɗa ya ce, aikin wanda gwamnatocin baya suka gaza kammalawa ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen gwamnatinsa.

“Daga sanya hannu a wannan kwangila, za mu ba su kashi 40 cikin 100 na wannan kuɗaɗe, wanda ya kama wajen biliyan 11 da wani abu domin kada aikin ya tsaya,” in ji gwamnan a lokacin ƙaddamar da aikin.

Ya ƙara da cewa daga nan za a ci gaba da biyan kuɗin har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

Shugaban hukumar samar da ruwan sha ta Katsina, Tukur Hassan, ya ce an tura ma’aikata zuwa ƙasashen Zambia da Rwanda da Jamus da Afirka ta Kudu domin samun horo kan yadda za su riƙa kula da tashar.

Ƙananan hukumomin da za su amfana da shirin su ne Kankiya da Ɓatagarawa, da Katsina da Rimi da Caranci da kuma DutsinMa.

By ukarofi