
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kogi, CP Naziru Kankarofi ya jagoranci ƙarin matsayi na wasu jami’ai su guda 42 a jihar inda ya jaddada ƙoƙarinsu na ƙwarewa akan lamuran tsaro.
A ranar Talata, rundunar ƴan sandan jihar ta yi bikin ƙarin matsayin jami’an a muƙamai daban-daban, waɗanda daga cikinsu akwai jami’in hulɗa da jama’a, SP William Aya a hedikwatar rundunar da ke Lokoja.
Da yake jawabi, CP Kankarofi ya taya jami’an murna bisa samun ƙarin girman, sannan ya yi kira a gare su da su yi amfani da hakan wajen inganta ayyukansu a ko’ina suka tsinci kansu.
Ya ce, akwai buƙatar a samu ladabtarwa da aiki bisa ƙwarewa a tare da su da damawa da jama’ar gari wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
Haka kuma ya yi godiya ga Sufeto Janar Kayode Egbetokun; Shugaban Hukumar Kula da Ƴan sanda, Alhaji Hashimu Argungu (Rtd) bisa gagarumar gudumawarsu da fifita walwalar ƴan sanda, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda zai ƙara wa jami’ansu karsashi yayin gudanar da ayyukansu.
A nasa jawabin, mai ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsaro, Komodo Jerry Omodara ya yaba da nasarar aiki da rundunar ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatin jihar ta cigaba da ba ƴan sanda goyon baya da tallafin da suke buƙata a ƙoƙarinsu na kiyaye doka da oda.
