Yanzu-yanzu: Kotu za ta yi shari’ar Nnamdi Kanu 20 ga Nuwamba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana 20 ga watan Nuwamba, 2025 a matsayin ranar yin shari’ar zargin ta’addanci ta tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Mai Shari’a James Omotosho yayin gabatar hukunci akan lamarin a yau Juma’a ya sanar da hakan bayan kwanaki shida da aka ɗiba wa Kanu na gabatar da hujja akan abinda ake tuhumar sa akai na ta’addanci sun ƙare.

Alƙalin ya ce, duba da cewa ya gaza amfani da damar da kotun ta ba shi na ya kare kan nasa, daga yanzu bai da hujjar cewa an tauye masa ƴancin da doka ta ba shi na kare kai.

A ranar Laraba Kanu ya ƙi fitar da hujjarsa akan tuhume-tuhume akansa guda bakwai da aka gabatar masu alaƙa da ta’addanci, waɗanda Gwamnatin Tarayya ta shigar.

A zama da aka yi a baya, Kanu, wanda shi ne yake kare kansa a kotun, ya ce duk abubuwan da ake tuhumar sa da aikatawa ba su halasta ba a dokance kasancewar suna daga cikin hukunce-hukuncen doka da aka soke.

Ya zargi kotun da saɓa wa hukuncin Kotun Ƙoli da ya yi watsi da ɗauko shi daga Kenya da kuma neman alƙalin ya gaggauta sallamar sa.

Baya ga haka, Alƙalin ya roƙi Kanu da ya shawarci lauyoyin da ke kare a baya, wato Aloy Ejimkor, Nanaemeka Ejiofor, Maxwell Okpara da Mandela Umegborogu da nufin su tsaya masa wajen gabatar da hujja, lamarin da Kanun ya amince wa.

By Babaji