Kamfani ya ƙirƙiri fasahar AI don sa ido kan zaɓe a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin fasahar zamani na SoftSmart Enterprise Solutions ya ƙaddamar da sabuwar na’ura mai amfani da AI domin bibiyar sahihancim zaɓe da sakamakon zaɓe, da nufin ƙara gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe a Nijeriya.

A wani taron manema labarai a Abuja, Daraktan Kamfanin, Charles Yakubu, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin “babbar nasara” wajen tabbatar da sahihin zaɓe a ƙasar.

Ya ce tsarin yana amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI da Optical Character Recognition (OCR) domin gane bayanan sakamakon da aka ɗora a IReɓ na hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC.

Na’urar za ta karanta sakamakon Form EC8A kai tsaye, ta tantance su, sannan ta tura su cikin babban ma’ajiyar bayanai domin samar da allon sakamako kai tsaye da kowa zai iya gani.

Yakubu ya ce, fasahar za ta iya gane takardun sakamako cikin daƙiƙoƙi 30 da kusan 95% inganci, yana mai cewa hakan ya yiwu ne ta hanyar ci gaban fasaha a fannin hangen hotuna da AI.

“Wannan fasaha za ta samar da abin da na kira gane sakamako a fili, kowa na gani a lokaci guda,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, fasahar za ta taimaka wa ‘yan ƙasa, jam’iyyun siyasa da masu sa ido su bi diddigin sakamako daga rumfar zaɓe zuwa matakin gunduma da ƙaramar hukuma.

Yakubu ya ce, kamfanin zai nuna cikakken gwajin tsarin a lokacin zaɓen gwamna na 8 ga Nuwamba a Anambra, inda za a riƙa ganin sakamakon a fili yayin da ake loda shi.

Ya bayyana wannan aiki a matsayin ƙari ga tsarin INEC, wanda zai inganta gaskiya, ya sa a riƙa samun amincewar jama’a, kuma ya taimaka wajen hanzarta sanin halin da zaɓe ke ciki, kamar yadda ake gani a ƙasashen waje.

Kamfanin SoftSmart Enterprise Solutions dai kamfani ne na Njjeriya da ke ƙwarewa a fannin tsarin AI a fannin gudanar da mulki da kuma tsarin zaɓe.

By ukarofi