Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙarshen makon nan ne mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi Honarabul Sama’ila Muhammad Bamboo ya sami kan sa bayan kwashe sama da sati ɗaya hannun masu garkuwa da mutane da suka tafi da shi tun ranar Juma’ar da ta gabata.
Bayanai daga fadar gwamantin jihar ta Kebbi sun bayyana cewa an sako mataimakin Kakakin majalisar ne a ƙarshen makon nan sai dai babu wani cikakken bayani dangane da ko an kai kuɗin fansa ko kuma nawa ne aka kai don fansar sa.
Bayanan dai sun nuna cewa yanzu haka dai yana wata asibiti da ita ma ba a bayyana ba inda likitoci suna duba lafiyar sa.
Wata mai kama da wannan shi ma Alhaji Abubakar Chindo ) Dan madamin.Bunza) wanda jami’in gudanar da lamurran siyasar tsohon gwamnan Kebbi kuma Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Sanata Muhammad Adamu Aliero ya shaki iskar yanci bayan da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da shi kwanan baya, bayan da suka karɓi kudi sama da naira miliyan talatin (#30, 000,000) da kayan abinci da suka haɗa da Indomie da kiret-kiret na ƙwai da katin waya da dai sauran kaya.
Haka-zalika bayanai daga garin na Bunza sun nuna cewa yan siyasa da yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati duk suna nan suna hijira daga garin zuwa garin Birnin Kebbi zuwa babban birnin jihar yayin da waɗansu kuma suka koma wasu manyan garuruwa.
