Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ƙungiyoyi farar hula (CSOs) na Jihar Yobe sun gudanar da zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci Women-Led Network of Civil Society Organisations, a wani muhimmin mataki da ya zama tarihi tun bayan kafa wannan ƙungiya mai ƙarfafa jagorancin mata a jihar.
Zaɓen ya samu halartar ƙungiyoyi daban-daban masu jagorancin mata daga sassan jihar, inda aka bayyana shi a matsayin sabon babi wajen ƙarfafa jagorancin mata, haɓaka haɗin kai, da kuma faɗaɗa murya ɗaya a fagen ci gaban al’umma da shugabanci.
A cikin saƙon taya murna da ta fitar, tsohuwar sakatariya ta ƙungiyar, Fatima Mohd Paga, ta yaba da yadda mambobin suka gudanar da zaɓen cikin lumana, haɗin kai, da fahimtar juna.
“A matsayina na tsohuwar sakatariya, ina alfahari da irin ci gaban da muka samu wajen kafa ginshiƙi mai ƙarfi na fafutuka, haɗin kai da ƙarfafa mata. Ina da tabbacin cewa sabbin shugabannin za su ci gaba daga inda muka tsaya kuma su kai ƙungiyar mataki mafi girma,” in ji ta.
Sabbin shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da: Amina Abdullahi Abubakar Mataimakiyar babbar darakta, Maryam Hassan Gambo sakatariya, Aishatu Tijjani mataimakiyar sakatariya.
Bintu Musa – daraktar harkokin shari’a, Hauwa Sule Mamudo – daraktar hulɗa da hama’a, Fatima Musa Auwal – daraktar jinsin mata da haɗa kan jama’a, Maryam Suleiman Yalwa daraktar ilimi, tashin hankalin jinsi da kare yara, Queen Amina Yusuf Auta – daraktar fafutuka da haɗin gwiwa Fatsuma Nasiru daraktar lafiya, ruwa, tsabtace muhalli da rayuwa Rhoda Layi, ma’ajiyar kuɗi.
Paga ta shawarci sabbin shugabannin da su ci gaba da gudanar da jagoranci bisa gaskiya, adalci, da haɗin kai domin ciyar da ƙungiyar gaba, tare da mai da hankali wajen kare haƙƙin mata da yara da kuma tabbatar da daidaiton jinsi a matakai daban-daban.
“Ina taya sabbin shugabannin murna bisa wannan nasara, kuma ina fatan Allah ya ba su ikon gudanar da jagoranci mai cike da tasiri da ci gaba ga mata da al’ummar Jihar Yobe baki ɗaya,” in ji ta.
Women-Led Network of Civil Society Organisations na Jihar Yobe na ci gaba da zama wata muhimmiyar dandalin haɗin kai da goyon bayan ƙungiyoyin mata wajen tabbatar da adalci, daidaiton jinsi, da kuma ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.
