Malam Nata’ala: Ko Kannywood ta yi masa hallaci?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitaccen jarumin Kannywood, Yakubu Mato, wanda aka fi sani da sunan “Malam Nata’ala”, ya rasu a daren Lahadi, 2 Nuwamba 2025, a Asibitin Jami’ar Maiduguri, bayan ɗaukar lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya. Wannan babban rashi ne ga masana’antar Kannywood da kuma al’umma baki ɗaya, musamman a Arewacin Najeriya.

Malam Nata’ala ya shahara ne a matsayin jarumin barkwanci wanda tauraruwar sa ta haskaka a lokacin da aka ya fara fitowa a cikin shirin Dadin Kowa, inda ya fito a matsayin malamin almajiri mai barkwanci, wanda ya ja hankalin masu kallo da dama tun daga shekarun farko na Kannywood. Rawar da ya taka ta kasance ginshiƙi wajen bunƙasa nishaɗi mai ɗauke da darasi, wanda ya haɗa ilimi, tarbiyya da barkwanci cikin fina-finai da shirye-shirye na talabijin.

Rahotanni sun nuna cewa, tun a farkon rashin lafiyarsa masoya da abokanain sana’ar tasa sun nuna damuwa matuƙa kan ciwon nasa, inda wasu daga cikin ‘yan fim suka gudanar da tarukan tallafi domin taimaka masa wajen samun magani. Haka ma an ruwaito cewa, Kannywood Vanguard ta taka muhimmiyar rawa wurin kafa wa Malam Nata’ala gidauniya don tara masa kuɗaɗe, a ƙoƙarinsu na samar masa abinda zai yi hidimar lalurar da ta same sa ta jinya.

Wannan yunƙuri da group ɗin Kannywood Vanguard wadda ke ɗauke da jarumai da kuma ma’aikan Kannywood ta kowane ɓangare suka yi ya haifar da ɗa mai ido, kuma abin a yaba ne, domin ya samar da tallafin da ya zama sasauci ga marigayin.

Mambobi daga ƙungiyar MOPPAN tun daga shuwagabanni zuwa ‘yan ƙungiya sun saka abinda Allah ya hore a asusun wanda za mu iya cewa daga ƙarshe kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Wataƙila wannan yunƙirin nasu na ɗaya daga cikin dalilan da suka kai shi ga samun tallafi daga gwamnatin Jihar Yobe, wadda ta shigo ta tallafa masa. 

Hakazalika an ruwaito cewa, Shugaban ƙasar Nijar shi ma ya bayar da tallafin kuɗaɗe masu nauyi ga marigayin inda ya ce ya yi amfani da su don kula da lafiyarsa.

Da wannan za mu iya cewa, Malam Nata’ala na daga cikin jaruman da suka samu kulawa mai kyau daga masoyansa da kuma abokanain sana’arsa yayin rashin lafiya. 

Masana’antar fim da ‘yan wasan kwaikwayo sun bayyana cewa Malam Nata’ala ya taka rawa sosai wajen gina al’adar wasan kwaikwayo ta Hausa. Rawar sa ta barkwanci da ilmantarwa ta bai wa masu kallo dama su koyi darasi cikin nishaɗi, yayin da ya zama abin koyi ga matasa da sauran jaruman da ke tasowa a masana’antar.

Wannan ne ya sa muka dawo da tambayar da muka taɓa tattaunawa a can baya a wannan shafin namu ta shin me ke sa manyan jaruman fim maza na Najeriya ke ƙarewa da neman taimako bayan barin harkar fim ko rashin lafiya?

Kusan za mu iya cewa, ma’abota kallon fina-finan Hausa na da da kuma yanzu ɗaiɗaiku ne za su ce ba su san Malam Nata’ala ba, kasancewar ya fara fim tun shekaru masu yawa baya, kuma a ‘yan shekarun nan tauraruwarsa ta ƙara haskawa yayin da yake taka rawa a manyan fina-finai musamman wanda ya yi a tashar AREWA24, wanda ya samar masa masoya daga matasan zamanin nan, hakan ya sa shi a jerin dattawan da ake ribibin su a ɓangaren barkwanci. 

Wannan zai sa mai kallo tunanin cewa, fim ya masa riga da wando, kuma zai iya riƙe shi ko bayan ya bar harkar. 

Malam Nata’ala bai kasance jarumi na farko da ya fuskanci matsalar rashi a lokacin lalura ta ciwo ba, duk da cewa wasu na ɗora alhakin hakan kan ba wa harkar fim rayuwarsu gaba ɗaya da wasu jaruman ke yi ba tare da haɗa shi da wata sana’ar ba, a cewarsu sana’ar fim kawai ba ta iya riƙe mai yint, saidai ya kasance daga cikin jaruman da masana’antar Kannywood ta nuwa wa hallaci tare da tabbatar da suna kishin nasu.

An shirya jana’iza da taron makoki a cikin birnin Maiduguri, inda ‘yan fim da masoya suka hallara domin girmama rayuwar Malam Nata’ala. Rashinsa ya jawo tunani kan yadda masana’antar Kannywood za ta ci gaba da girmama waɗanda suka yi fice kafin su bar duniya, tare da ƙarfafa gwiwar sababbin taurari wajen ɗaukar nauyin bunƙasa al’adar nishaɗantarwa a Arewacin Najeriya

By ukarofi