Mahaifiyar Ministan Muhalli Abbas ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mahaifiyar Ministan Muhalli da Albarkatun Ƙasa, Mallam Balarabe Lawal Abbas, Hajiya Ɗayyabatu Lawal Aliyu ta rasu.

A yammacin jiya Lahadi ta rasu a gidanta da ke Zariya City a Jihar Kaduna.

Wata majiya mai kusanci da iyalanta ta shaida wa wakilinmu cewa ta rasu ne bayan fama da wani rashin lafiya.

Marigayar ta shafe shekaru 93 a duniya.

Wakilin namu ya ruwaito cewa za a yi jana’izarta a yau Litinin da misalin ƙarfe 11 na safe acikin garin Zariya.

By Babaji