Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi wani mataki ko magana kan shari’ar da ke gaban kotu ta shugaban ƙungiyar da aka haramta ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ba.
Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin hulɗa da al’umma na yankin Kudu maso Gabas, Chioma Wesley, ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, Abuja, a ranar Litinin, bayan ta da wasu mataimaka uku daga sauran yankuna sun yi wa Shugaban ƙasa bayani kan aikinsu.
Ta ce, “Shari’ar Nnamdi Kanu tana gaban kotu, kuma Shugaban ƙasa ba zai iya yin wata magana kai tsaye a kanta ba. Shugaban ƙasa na bin dokar ƙasa. Don haka muna jiran hukuncin kotu ne kawai.”
Wannan furuci nata na zuwa ne bayan ƙarin kira daga wasu sassan Kudu maso Gabas da ke neman a sake Kanu daga tsarewa.
An kama Kanu a karon farko a 2015, sannan aka ba shi bel a 2017, kafin daga bisani ya bar ƙasa bayan harin da sojoji suka kai garinsu na Afaraukwu, jihar Abia. Daga baya aka sake kama shi a watan Yuni, 2021, aka dawo da shi Nijeriya, kuma tun daga lokacin yana tsare a hannun DSS.
Kotun ƙoli ta Ƙasa ta sanya ranar 20 ga Nuwamba, 2025, domin yanke hukunci a shari’ar ta’addanci da ake masa, bayan ya ƙi buɗe kariyarsa karo na shida.
Wesley ta kuma bayyana cewa ofishinta na Kudu maso Gabas ya kafa wani tsarin “Citizens’ Assembly” domin haɗa jama’a kai tsaye da Fadar Shugaban ƙasa.
“Muna zuwa kai tsaye cikin al’umma domin yada manufofin Shugaban ƙasa da kuma jin ra’ayoyin mutane kan ayyukan da ake aiwatarwa. Muna tabbatar da cewa jama’a a ƙasa sun fahimci abin da Shugaban ƙasa ke yi musu,” inji ta.
Ta ƙara da cewa, mafi muhimmancin abin da suke dogaro da shi shi ne samun sahihan ra’ayoyi daga ƙasa — “feedback” — domin inganta tasirin manufofin gwamnati.
Ita kuwa mai wakiltar yankin Arewa ta Tsakiya, Dr. Abiodun Essiet, ta bayyana cewa sun kafa tsarin zaman lafiya a matakin ƙananan hukumomi 121 domin magance rikice-rikicen da ke jawo rashin jituwa a yankin.
“Mun kafa tsarin zaman lafiya a ƙananan hukumomi domin ƙarfafa haɗin kai da wanzar da zaman lafiya. A mako mai zuwa zan je Jihar Plateau domin ƙaddamar da wani tsarin makamancin haka. Za mu haɗa shugabannin addinai, ƙungiyoyin makiyaya da manoma, sarakuna, da ƙungiyoyin matasa domin zama a kan shafi ɗaya game da zaman lafiya,” inji ta.
Ta danganta yawaitar rashin tsaro a yankin da tsofaffin matsalolin rashin amincewa da rashin kyawun hanyoyi, tana mai cewa wasu daɓe da daji a kan iyakar Kogi da Kwara sun zama mafakar ‘yan fashi saboda rashin hanyoyi masu kyau.
Ta ce, Shugaban ƙasa ya yi alƙawarin ƙarfafa waɗannan tsare-tsaren zaman lafiya, tare da kafa cibiyar sa ido a matakin al’umma domin daƙile rikice-rikice tun kafin su yi tsanani.
