Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta amince da kashe fiye da naira tiriliyan 1.04 domin gudanar da manyan ayyukan gina hanyoyi a sassa daban-daban na ƙasar.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ƙarshen mako, inda ya ce Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da wannan kuɗin ne a zaman ta na ranar 6 ga Nuwamba, 2025.
A cewar Umahi, cikin ayyukan da aka amince da su akwai: Sokoto–Badagry Coastal Superhighway (Sashen 3, daga Badagry zuwa iyakar Ogun–Oyo) mai tsawon kilomita 163, da za a gina gaba ɗaya da siminti, wanda zai ci naira biliyan 553 (N3.39bn/km); Ota–Idiroko (Sashe na I) a kan N98 biliyan, tare da gadar sama mai kuɗin biliyan N23.
Haka kuma, akwai Ijebu Igbo–Etapa–Owoyen Road mai tsawon kilomita 37 a kan N53 biliyan; Lagos–Ibadan Eɗpressway (Mataki na II, Sashe na II) wanda aka sake bayar da kwangila kan N43.73 biliyan, da ke haɗa wuraren tafiya ta ƙasa, gadar sama da hanyoyin gefe; sai kuma Ilorin–Omu Aran–Egba Road (Mataki na I) mai tsawon kilomita 31 kan N43 biliyan.
Sauran ayyukan sun haɗa da Wasasa–Turunku–Mararaba (Mataki na II) a Kaduna mai tsawon kilomita 42, akan N30.23 biliyan; Enugu–Onitsha Road (Mataki na I) daga OP Junction zuwa iyakar Anambra, mai tsawon kilomita 35, akan N28.47 biliyan; Mushin–NNPC–Apapa–Oshodi Dualisation (14.4 km) a Legas, wanda zai ci N19.09 biliyan; da kuma East–West Road (reshaped PH–Warri aɗis) wanda ya haɗa flyovers uku da gada biyu da aka gada daga tsohuwar kwangila, akan N156 biliyan.
Umahi ya bayyana cewa ƙarin kuɗin ayyukan ya samo asali ne daga sabbin ƙira, yanayin ƙasa mai wahala, da hauhawar farashin kayan gini, inda ya ce farashin ƙarfe (reinforcement steel) yanzu ya haura N1.1 miliyan kowace tan.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnonin jihohin Edo, Delta da Abia sun yarda su ɗauki nauyin kuɗaɗen gina wasu hanyoyin Tarayya da ke yankunansu, domin sauƙaƙa wa Gwamnatin Tarayya nauyin kashe kuɗaɗe da kuma hanzarta kammala ayyukan.
A cewar Umahi, “Waɗannan sabbin amincewa suna nuna jajircewarmu wajen samar da ingantattun hanyoyi masu ɗorewa, da aka gina da siminti, waɗanda za su iya ɗaukar shekaru da dama cikin aminci, tare da tabbatar da cewa an samu cikakkiyar moriya daga kuɗin gwamnati.”
