Ƙudirin hana ƴan ƙasa da shekaru 18 shiga aikin soja ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa na neman soke dokar da ta bada damar ɗaukar aikin soja ga waɗanda shekarunsu ya gaza 18, yayin da karatun buƙatar haka na ƙudirin 2025 ya tsallake karatu na biyu a wajenta.

Sashen ƙudirin ya haramta wa ƙananan yara su shiga aikin soja bisa la’akari da kundin ƴancin yara na 2003 da dokokin ƴancin yara na Majalisar Ɗinkin Duniya da na Afirka.

Haka kuma, ƙudirin, wanda Sanata Abdulaziz Yar’Adua na Katsina ta Tsakiya ya ɗauki nauyi, ya nemi a soke sashen sojojin na 2004 da maye gurbinsa da wani kundi da dokokin ƙasa suka amince da shi.

Ya bayyana cewa, hukunce-hukuncen sojoji da ake amfani da shi a yanzu ya samo asali ne daga dokokin soji da ainihi tun zamanin mulkin soja, wanda a yanzu ya saɓa tsarin gwamnatin da ake tafiya akanta ta dimukraɗiyya.

Daga cikin abinda ƙudirin ya ƙunsa na gyare-gyare akwai faɗaɗa laifukan sojoji, gabatar da wasu sababbin hukunce-hukunce ga masu laifi da kariya ga ƴancin kotunan sojoji da dai sauransu.

Haka kuma gyaran zai ƙunshi bai wa jami’an sojoji da suak cancanta damar tsayawa su wakilci sojoji a kotunan fararen hula.

By Babaji