Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa, kan iyakar jihar tasa da Jamhuriyar Nijar ne ta haifar da matsalolin tsara a faɗin jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a lokacin da ya kai ziyara a cibiyar tsaron iyakoki ta ƙasar Belarus.
Babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan Muhammad Kaula ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya kai ziyarar ne domin neman haɗin gwiwa kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.
A yayin ziyarar, Gwamna Raɗɗa ya tattauna da jami’an cibiyar kan yiwuwar haɗin gwiwa a fannonin musayar bayanan sirri, amfani da fasahar zamani wajen sa ido a iyakoki, da kuma horas da jami’an Katsina Community Watch Corps (KCWATCH) da sauran hukumomin tsaro a jihar.
Nijar yana cikin abubuwan da suka haifar da ƙalubalen tsaro da suka haɗa da ta’addanci, safarar makamai, da fataucin mutane wanda a cewar gwamnan matsalar na buƙatar haɗin kan ƙasa da ƙasa da kuma amfani da fasahar zamani wajen magance su.
Cibiyar tsaron iyakoki ta Belarus ta bayyana shirinta na ba da goyon baya ga Jihar Katsina ta hanyar tallafin fasaha da gina ƙwarewar jami’an tsaro.
Gwamna Raɗɗa ya ce wannan hadin gwiwar na da cikakkiyar alaƙa da ƙudirin gwamnatinsa na inganta harkokin tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ƙarƙashin shirin sa na “Building Your Future.
Matsalar tsaro na cimma gwamnatin Katsina tuwo a ƙwarya domin a halin yanzu ‘yan bindiga da su kai shekara ta shekaru sun cin karen su ba babbaka.
Gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kashe biliyoyin Naira wajen samar da tsaro a jihar amma har yanzu matsalar ba ta kau ba.
