Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sun kai ziyarar na kwanaki uku domin samun ƙarin horo da musayar bayanai da kuma ƙarfafa alaƙar aiki da hukumar LASTMA, me Kula da ababen hawa da dokokin tuƙi a jihar.
Ita LATSMA ta shafe sama da shekaru 25 tana gudanar da ayyukan kula da zirga-zirga da tilasta ma masu ababen hawa bin dokokin tuƙi a jihar Legas tun lokacin mulkin Bola Tinubu yana gwamnan jihar.
Jami’an KASSAROTA da suka halarci taron bitan sun haɗa da Shugaban hukumar, Manjo Yahaya Garba Rimi (Rtd.), Sakataren Hukumar, Aminu Lawal Al-amin Batsari , Kwamanda Alh. Dahiru Mani Bagiwa, da jami’in hulɗa da jama’a, Abubakar Marwana Kofar Sauri.
Ziyarar ta bai wa KASSAROTA damar nazarin samun cigaba, tare da nemo hanyar magance ƙalubalen da yake faruwa a lokachin da suke gudanar da aikin su, fahimtar irin dabarun da LASTMA ke amfani da su, domin inganta tsarin sufuri, rage haɗurra da ƙara tsaro a jihar Katsina baki ɗaya.
Wannan yunƙuri yana daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Dikko Raɗɗa na sauya fasalin gudanar da harkokin zirga-zirga da tabbatar da kiyaye dokokin hanya da rage haɗurra tare da cigaban jihar Katsina.
Shugaban hukumar KASSAROTA a Katsina Manjo Garba Yahaya Rimi a jawabin da yayiwa manema labarai kafin tafiyar su Legas,ya sanar da cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya amincewa hukumar ta kafa cibiyar gane ababen hawa da bayanai a kan su wanda ya ce haka zai inganta tare da ɗaukaka aikinsu.
Manjo Yahaya ya bayyana cewa abubuwan da suka gani da waɗanda suka koya zai taimaka ma hukumar ta fito da tsare tsare da suka shafi aiwatar da sabbin dokokin hanya,da kula da zirga-zirga na ababen hawa ta hanyar amfani da yanar gizo a jihar Katsina.
Ya sanar da cewa a ƙoƙarin hukumar na faɗaɗa aikin ta,ta ƙara ɗaukan ma’aikata tare da ƙirƙiro ƙarin ofishin ta da ke shiyoyi uku da ke Katsina, Daura da Funtua
Zuwa 15 domin samun damar shiga lungu lungu na faɗin jihar domin ganin masu ababen hawa sun bin ƙa’idojin hanya.
