Abinda ya sa Nijeriya ba za ta iya samar da rigakafi ba – Minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙaramin Ministan Lafiya, Iziaq Salako ya ce har yanzu Nijeriya ba ta kai matsayin da za ta riƙa samar da rigakafin cututtuka a ƙasar ba bisa la’akari da matakin ƙarfinta.

Salako ya bayyana haka ne a wata hira ta gidan talabijin na Channels a jiya Alhamis inda yake bayyana matakin ƙarfin Nijeriya game da samar da rigakafi.

Ya ce, samar da rigakafi abu ne da ke buƙatar a yi la’akari da ƙarfin tattalin arziƙi da kayan aiki, lamarin da a cewarsa ke da buƙatar ɗaukar ɗawainiyar kansa yayin da aka fara.

Ya ƙara da cewa, a yanzu haka Nijeriya tana da mutane sama da miliyan 240 wanda hakan ƙarfi ne na musamman, saidai wajibi ne fannin ya dace da tsare-tsaren duniya.

Kazalika, Ministan ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa fannin lafiya a ƙasar yana nan da ƙarfinsa wajen tunkarar dukkan ƙalubalen annoba da ake fuskanta a duniya.

A ƙarshe, ya bayyana cewa shirin Nijeriya na tunkarar annoba ya ƙara ƙarfi a yanzu, yana mai gargaɗin al’umma da su riƙa ƙaurace wa yin magani ba tare da shawarwarin likitoci ba.

By Babaji