A cikin wannan zamani da rayuwa ta zama cike da ƙalubale da sauye-sauye, muna ganin wani hali mai tayar da hankali — na wasu mata da ke raina mazajensu. Wannan wasiƙa ba don cin zarafi ba ce, amma don faɗakarwa da gargaɗi; domin kamar yadda ake ja kunnen maza masu dukan mata, haka ma wajibi ne a ja kunnen mata masu wulaƙanta mazajensu.
A kwanakin nan, wani dattijo ya kira ni a waya cikin murya mai cike da takaici da raɗaɗi. Ya ce: “Don Allah ka rubuta wata wasiƙa ta kira ga mata masu raina mazajensu. Ni idan banda tsoron Allah, da ban san iya adadin sau nawa na doke matata ba. Amma na ɗauki matakim haƙuri tsawon shekaru fiye da talatin da biyar, duk da yadda take raina ni tana kuma nuna kamar ni ba mutum ba ne.”
Wannan magana ta sa na yi dogon tunani. Shekaru 35 ba wasa ba ne. Rayuwar aure tana da tsawo, tana buƙatar haƙuri, girmamawa, da mutunta juna. Amma abin takaici, a wasu gidaje, mace tana ɗaukar matsayin da bai dace ba – tana kallon mijinta kamar ƙaramin abu, tana raina shi, tana zagin shi a gaban ‘ya’yansu, har ma wasu suna wulaƙanta mazajensu saboda kuɗi ko matsayi.
A yau, wannan wasiƙa tana fita ne ga mata — musamman waɗanda suka manta cewa aure ba fili ba ne na gwaji, ko wurin nuna isa, ko damar danniya. Aure gandu ne na mutunci da biyayya. Idan mace ta manta da wannan, tana karya ginshiƙin da ya kafa rayuwar aurenta.
Aure amana ce tsakanin mutum biyu — namiji da mace — kuma amana tana buƙatar biyayya, fahimta, da girmamawa. Wasu daga cikin matan sun fara kallon mazajensu kamar abokan hamayya maimakon abokan tafiya. Sun daina ganin darajar aure, suna kallon gyara da nasiha a matsayin tsangwama. Wannan yanayi yana iya haifar da ɓarna da rushewar gidajen aure.
A cikin Alƙur’ani mai girma, Allah Ta’ala Ya faɗa: “Ku zauna da su cikin alheri.” (Surat An-Nisa’i: 19). Wannan ayar ba ta nufin mace ta yi watsi da haƙƙinta ba; tana nuni ne ga mahangar tausayi da ladabi a dangantaka.
Annabi Muhammadu (SAWW) ya ƙara da cewa: “Mafi alherin ku shi ne wanda yafi kyautata wa matarsa.” Idan jagoran addini bai taɓa dukan mace ba, to ya kamata mu fahimci cewa rashin tashin hankali shi ne tafarkin nagarta.
Raini na iya zama guba mai lalata zuciyar miji fiye da duka. Wasu maganganu da ake yi cikin fushi kamar “ba kai ne ke ciyar da ni ba” (saboda Allah ya jarabci miji da rashin kuɗi), ko “zan iya rayuwa ba tare da kai ba,” ko zagin miji a gaban ’ya’ya suna rage mutunci, suna gina banbanci, kuma suna barin tabo a zuciyar aure. Irin wannan hali yana sanya yara su koyi rashin girmama mahaifi, ya haddasa rabuwar kai, kuma a ƙarshe zai iya janyo rushewar gida.
Mace mai hankali tana iya tsayawa ta nuna rashin jin daɗinta ba tare da cin mutunci ba. Idan akwai matsala, tattaunawa cikin natsuwa, neman shawarar dattawa ko malamai, ko neman sulhu ta hanyoyin addini da na al’ada sun fi dacewa da amfani fiye da cin mutunci a fili. Biyayya ba wulaƙanci ba ce; ita ce hanya ta gina gida mai ƙarfi.
Wasu mata suna ɗauka cewa bin miji da girmama shi yana nufin rashin ’yanci. A’a. A Musulunci, bin miji da mutunta shi ibada ce idan aka yi da gaskiya.
Manzon Allah (SAWW) ya ce: “Idan da zan umarci wani ɗan adam ya yi sujada ga wani, da na umarci mace ta yi sujada ga mijinta, saboda girman haƙƙinsa a kanta.”
Wannan ba yana nufin mace ta zama baiwa ba ce, amma yana nufin ta gane cewa aure tsari ne da yake buƙatar ladabi da biyayya. Girmama miji ba yana rage darajar mace ba ne, sai ma ƙara mata daraja a gurin Allah Ta’ala da gaban al’umma da kwanciyar hankali.
Aure ba ya ɗorewa idan babu girmamawa. Lokacin da mace ta saba da raini, tana zagin mijinta ko tana kallon sa da wulaƙanci, to tana lalata kansa da kuma lafiyar gidanta. Wasu maza suna shiga damuwa, suna rasa kwarin gwiwa saboda kalaman raini da cin fuska daga matansu.
Wani mai hikima ya ce: “Maganganun mace sukan iya sara fiye da takobi.” Wannan gaskiya ce. Kalmar da mace ta faɗa cikin fushi na iya rushe soyayya da aka gina cikin shekaru masu yawa.
Mutumin da ya kira ni ya ƙara da cewa: “Na yi haƙuri saboda Allah. Amma duk da tsawon shekarunmu tare, har yau tana gani kamar bata da abin godiya gare ni.”
Wannan irin magana tana ƙuna a zuciya. Domin a gaskiya, miji da mata duk suna da haƙƙoƙi, amma idan mace ta manta da ladabi, tana tozarta kanta da kanta.
Wasu mata ba sa sanin irin haƙurin da mazansu ke yi. Su na iya faɗa masa kalmomin da ba su dace ba, su ƙi masa girki, su yi wulaƙanci a gaban yara, amma shi ya yi shiru. Wannan shiru ba laifi ba ne ba kuma tsoro ba ne, amma alamar mutunci da tsoron Allah ne. Duk da haka, ya kamata mata su daina amfani da wannan haƙuri wajen cutar da mazajensu.
Idan ba don tsoron Allah ba, da wasu maza sun riga sun lalata gidajensu saboda irin wannan raini. Amma saboda tausayi da imaninsu, suna ɗaukar haƙuri. Mace mai hankali ta kamata ta gane wannan, ta daina ɗaukar haƙurin mijinta a matsayin rauni.
Mace ta tuna cewa, duk abin da take yi a gidan mijinta, akwai lada ko zunubi. Idan ta bi mijinta da mutunci, ta taimake shi, ta girmama shi — to Allah zai saka mata da alheri. Amma idan ta raina shi, ta zubar da mutuncinsa, to tana tara zunubi mai nauyi.
Aure ba wasa ba ne. Ba abin gwaji ba ne. Kuma ba gasar iko ba ce. Miji da mata suna da nauyin gina juna, ba rusa juna ba. Idan mace ta daina ganin darajar mijinta, to ta riga ta buɗe ƙofar hakakarta.
Mata, ga shawara:
Ku daina kallon mazajenku kamar ba su isa ba. Ku tuna cewa shi ne mutumin da kuka zauna da shi shekaru da dama, wanda kuka yi aure da shi da alƙawarin zama tare cikin farin ciki da ƙunci. Idan yana da rauni, taimaka masa, ba raini ba. Idan yana cikin damuwa, kwantar masa da hankali, ba ƙara masa ba.
Idan mace ta yi wa mijinta addu’a, ta nuna masa soyayya da girmamawa, to hakan yana haifar da sakamako mai kyau a gidanta da kuma ga ‘ya’yanta. Amma idan ta zama mai tsayayya da raini, ‘ya’yanta ma za su koya hakan.
Wannan wasiƙa kira ce ga mata — musamman wazanda suka manta cewa aure ibada ce, ba wasa ba. Idan Allah ya ba ki miji, to ya ba ki shugaba. Idan kin mutunta shi, Allah zai mutunta ki. Idan kin raina shi, to ke ki ke jawo ƙarshen zaman lafiya a gidanki.
Wannan wasiƙa ba ta goyon bayan maza masu tashin hankali ko dukan mata ba. Manufar shi ne neman daidaito. Idan an ja kunnen namiji da mace game da miyagun halaye, to duka biyu suna da haƙƙin a tunatar da su game da nauyin da suka ɗauka. Dole ne al’umma, iyalai, da hukumomi su yi aiki tare wajen wayar da kai; malaman addini su yi wa mutane tarbiyya; ƙungiyoyin mata su tallafawa juna wajen ilmantarwa kan haƙƙin aure.
A ƙarshe, ga mata masu irin wannan hali: ku tsaya ku yi tunani — shin raini zai kawo farin ciki ko arziki? Shin girmamawa ba zai fi kawo zaman lafiya ba? Ku san cewa harshen mace na iya gina gida ko rushe shi. Ku zamo mata masu hikima, masu natsuwa, masu girmama mazansu. Ku tuna cewa aure ba filin ƙarfi ba ne; makaranta ce ta fahimta, haƙuri da tausayi. Idan akwai abin da ke damun ku, ku nemi hanyar gyara cikin ladabi — tilas ku sani cewa wannan hanya ce mafi tasiri.
Ga dattijon da ya kira ni — Allah ya saka maka da alheri bisa haƙurinka. Rayuwa tana cike da jarrabawa, kowa da irin tasa, kuma haƙuri shi ne makamin nagartattun maza. Amma wannan wasiƙa za ta ci gaba da zama tunatarwa ga mata masu raina mazajensu: Ku gyara halinku kafin ku kafin ku je gaban Allah!
Allah Ya sa gidajenmu su cika da tsoron Allah, soyayya, fahimta da zaman lafiya. Ilahee Ya Mujeeb.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD, ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.
