Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar Sojin Nijeriya ta fitar da hoto a hukumance na sabon Babban Hafsan Sojin ƙasa na ƙasa na 25, Laftanar Janar Waidi Shaibu, tare da gargaɗin manema labarai da jama’a su sabunta kundinsu na hoto kuma su daina amfani da tsofaffin hotuna a yayin wallafa labarai.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na hukuma a ranar Talata, an bayyana cewa wannan mataki na da nufin daidaita hoto da wakilcin Babban Hafsan Soji a kafafen watsa labarai da kuma kawar da ruɗani da amfani da hoton tsohon matsayi ke janyowa.
“Akwai buƙatar ku sabunta kundin hotunanku na kafafen yaɗa labarai kuma ku daina amfani da tsofaffin hotuna, musamman waɗanda ke nuna Babban Hafsan Sojin ƙasa a matsayin Manjo Janar,” inji sanarwar.
Rundunar ta kuma jaddada cewa hoton hukuma da aka fitar da farko ya zama abin watsi, domin manufar ita ce tabbatar da daidaito a dukkan kafafen labarai da takardun hukuma.
“Bugu da ƙari, ku share hoton farko da muka fitar ta wannan hanya,” sanarwar ta ƙara da cewa.
Sojin Nijeriya sun yabawa ƙwararrun ‘yan jarida bisa sahihin aikin da suke yi da goyon bayan da suke baiwa rundunar wajen isar da manufofin tsaron ƙasa cikin gaskiya da nauyi.
“Rundunar Soji na Nujeriya na godiya bisa ƙwarewa, sadaukarwa, da gagarumar gudunmawar da kuke bayarwa wajen watsa sahihan rahotanni game da ayyukanmu domin tabbatar da tsaro a ƙasa,” in ji su.
A tun da farko, an naɗa Laftanar Janar Waidi Shaibu a watan da ya gabata a matsayin Kwamandan Sojin ƙasa na 25, bayan babban sauyin shugabanci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ɓangaren tsaro.
Fitar da wannan hoto a hukumance na nufin tabbatar da matsayinsa na yanzu da matsayin da yake riƙe da shi, tare da samar da hoto daidai da matsayinsa ga jama’a da kafafen labarai.
