Kungiyar ’Yan Kasuwar Zamani ta Bichi ta kai ziyarar faɗaɗa harkokin kasuwanci a Kano

Spread the love

Daga WAKILINMU

Kungiyar ’Yan Kasuwar Zamani ta ‘Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited’ ta gudanar da ziyarar musamman a Kano domin faɗaɗa ilimi da dabarun kasuwanci, tare da neman haɗin gwiwa da hukumomin jihar wajen bunƙasa harkokin tattalin arziki a yankin Bichi.

A yayin ganawar da suka yi da Shugaban Hukumar Zuba Hannun Jari da Kula da Kadarorin Gwamnatin Kano, Hon. Auwalu Muntari Mai Royal, shugaban ƙungiyar, Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya bayyana jin daɗin tarbar da suka samu, tare da yabawa shawarwarin da aka ba su don inganta harkokin kasuwanci a Bichi.

Alhaji Mazahim ya bukaci ’yan kasuwa da su rubuta bukatunsu domin a duba su ta fuskar ƙwararru, musamman wajen tsara hanyoyin magance matsalolin kasuwa da samar da dabarun faɗaɗa harkoki.

Ya ce dole ne su haɗa hikimar kasuwanci da shawarwarin gwamnati domin ganin Bichi ta ci gaba.

Ya ƙara da cewa, “Idan ba mu gyara ƙasa ba, sama ba za ta gyaru ba. Mu haɗa kai, Allah da taimakonku za mu magance matsalolin, mu inganta kasuwa, mu samar da maslahar da za ta ƙara haskaka kasuwancin Bichi.”

A nasa ɓangaren, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Tsaftar Muhalli, Hon. Abdullahi Shehu Bichi, ya karɓi tawagar a ofishinsa na Audu Bako Secretariat, inda ya yaba da yadda ƙungiyar ke neman ci gaba. Ya yi alƙawarin tallafa musu wajen tsaftace muhalli, inganta magudanan ruwa da feshin maganin sauro a cikin kasuwar Bichi.

Ya ce, “Idan muka haɗa kai, za mu nemi damar shiga da na’urar share ƙazanta ta musamman domin tsaftace kasuwar gaba ɗaya.”

ƙungiyar ta kuma kai ziyara ga Mai Bai wa Gwamna Shawara kan ’Yan Fansho, kuma Shugaban Kwamitin Dattawa na NNPP, Hon. Abdullahi Shu’aibu (Kosi), kwararren masani a fannin harkar ƙasa da gidaje. A nan ma sun samu shawarwari kan yadda za a ɗaga darajar kasuwar ta fuskar kimar shaguna da tsarin kyautata haya.

Kosi ya bayyana cewa, ƙauyukan da ke kewaye da Bichi za su taimaka wa kasuwar idan an ƙarfafa su su dawo cikin gari don gudanar da harkoki, domin hakan “na ɗaga arziki, na kuma faɗaɗa tattalin arzikin gari.”

A wani ɓangare na ziyarar, ƙungiyar ta gana da Shugaban Gudanarwa na bankin Emaar Microfinance Bank, Alhaji Haruna Shehu, tare da H.O.D na bankin, Malam Rabi’u Yahaya Yakasai. Sun tattauna batutuwan da suka shafi samun damar kuɗaɗen jari, faɗaɗa sana’o’i da inganta tsarin kuɗaɗen kasuwanci a Bichi.

Daga nan ne ƙungiyar ta kammala ziyarar da tuntubar tsohon Shugaban Ma’aikatan ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Mahmud Faruk, a gidansa da ke Kabara, Kano. Faruk, wanda yanzu ke aiki a Hukumar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyarar tare da yi musu fatan alheri da ci gaba.

By ukarofi