Tattalin Arzikin Nijeriya na buƙatar sabon tsarin haraji — Shugaban FIRS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (FIRS), Dr. Zacch Adedeji, ya ce shirin sauya fasalin tsarin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta shi ne ginshiƙin da zai samu nasarar farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya a wannan lokaci na matsin lamba da raguwar kuɗaɗen shiga.

Da yake jawabi a taron farko na ‘Distinguished Lecture Series’ a Jami’ar Ilesa da ke Osun, Adedeji ya bayyana cewa matsalolin kuɗaɗe da Nijeriya ke fuskanta ba rikici ba ne, illa wata dama ta aiwatar da gyare-gyare masu zurfi domin ƙarfafa tattalin arziki.

A cewarsa, muhimmancin sauye-sauyen ya samo asali ne daga ƙalubalen duniya — daga tangarɗar dijital, hauhawar basussuka, sauyin yanayi, zuwa girgizar tattalin arzikin ƙasashe — waɗanda ke matsa lamba ga ƙasashen da ba su da tsarin haraji mai inganci.

A cikin laccarsa mai taken “Economic Resilience in an Era of Dwindling Revenue,” Adedeji ya jaddada cewa hanyar da ta dace ga Nijeriya ita ce: Gina ƙwararrun cibiyoyi, Faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗe, da zamanantar da tsarin haraji domin ɗorewar tattalin arziƙi.

Ya lissafa tushen ginshiƙai huɗu da Nijeriya za ta dogara da su wajen gina tattalin arziki mai ɗorewa, 1. Sauyin tsarin kuɗi (Fiscal fleɗibility), 2. Daidaiton manufofi (Policy coherence), 3. ƙarfafa cibiyoyi (Institutional strength) da 4. Haɓaka ƙwarewar ma’aikata (Human capital adaptability).

Adedeji ya bayyana cewa ƙara yawan kuɗaɗen da ba na man fetur ba, zurfafa sauya haraji, da saka jari a ilimi da fasahar zamani sune ginshiƙan da za su taimaka Nuijeriya ta daidaita da matsin lambar da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

A cewarsa, waɗannan matakan za su samar da inganci, gaskiya, da ƙara bin doka wajen biyan haraji.

Shugaban FIRS ɗin ya kuma yi kira ga jami’o’in Nuijeriya da su shiga cikin aikin gina sabon tsarin tattalin arziƙi, yana mai cewa jami’o’i na da rawar gani wajen ƙirƙirar tsare-tsare bisa bincike — da suka haɗa da harajin dijital, tsarin tara kuɗaɗe, da haɓaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Ya bayyana jami’o’i a matsayin tushen ƙirƙire-ƙirƙire da za su iya taimakawa wajen tsara manufofi da ƙara gasa ta tattalin arziki tsakanin ƙasashe.

By ukarofi