
A ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin al’ummar jihar Kano sun mayar da hankali wajen yin rijistar haihuwa, musamman ga yara kasa da shekara ɗaya da ake ci gaba da yi a fadin kasar nan, Karamar Hukumar Bichi ta duƙufa don tabbatar da wannan ƙudirin.
A Mazabar Fagolo, Bashir Abdullahi Usman, ya ce, bayan kammala bita da aka yi musu, aikin ya tafi yadda yakamata inda suka samu damar yi wa yara talatin rijistar ta hanyar bi gida-gida, amma sakamakon matsalar rashin network ya kawo tsaikon aikin a yanzu, sun kuma sanar da na gaba a gyara domin cigaba da aikin.
Ya ɗora da cewa, bangaren al’umma da ake yi wa wannan hidima suna bada hadin kai yadda ya kamata, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta bayyana.
“Mu na da yara. Kun yi musu? I an yi musu rijistar haihuwa. Har gida aka zo aka yi musu? An zo har gida an yi musu.” Jami’ar Yada Labarai ta karamar hukumar da Sadiya Mustapha Imam Fagolo.
“Aiki yana tafiya sosai tun da ana nan ana ta yi, yanzu mafi akasari ma yaran da muka samu dai-dai ne wadanda ba su da date of birth”, inji Hansa’u Ado Fagolo.
A mazaɓar Kwamarawa, jami’in aikin rijistar, Ibrahim Hamza ya shaida komai yana tafiya daidai, inda zuwa yanzu yake da adadin yara talatin da tara da ya yi wa rijistar.
Ya kuma ce, yanzu haka gab suke da zama da dagaci da masu unguwanni domin tsara yadda za a cigaba da wayar da kan jama’ar yankin tare da ranakun da kowace unguwa mutanenta za su rika zuwa a yi wa ‘ya’yan nasu rijistar, sannan ya tabbatar suna samun hadin kan al’umar yankin.
“Kina ganin mata suna ba da hadin kai wajen yin wannan rijistar? Sosai, ba laifi ana ta yi wa yara rijistar haihuwa. Gida-gida ake zuwa yi ko asibiti? Gaskiya asibiti ake zuwa.” Jami’ar Yada Labarai ta yankin da Malama Saratu Kwamarawa.
Haka jami’in rijistar haihuwar yara na Mazabar Saye, Abubakar Abdullahi, ya bayyana yara saba’in ya yi wa rijstar haihuwa, kuma yana gudanar da aikin ne ta hanyar bin sassan yankin daya bayan daya, inda yake kira ga dagaci da mai unguwa su yi kira ga al’umar yankunansu su fito domin yin rijistar.
Kalabalen da yake fuskanta, matsalar network a yayin tura bayanan yaro bayan kammala shigarsu.
“Dole uwar yaro ya zamto tana da katin dankasa, to kuma a wannan locallity namu ana samun wadan su iyayen ba su da wannan katin dankasar, saboda haka muna kira ga mai girma Ciyaman da kuma mai girma Gwamna a bude ko a samar da wata hanya da za a samar da wannan katin dankasar ga iyayenmu mata da suke zaune a wannan yanki namu.” Jami’in gudanar da aikin rijistar haihuwa na Mazabar Saye, Abubakar Abdullahi.
Dagacin Fagolo, Malam Habibu Adamu, Sarkin Fulanin yankin, wakilin dagacin Kwamarawa, Malam Garba Usman, dagacin Saye, Basiru Musa Magaji, sun yaba da tsarin yadda ake gudanar da rijistar kai waye sabanin ta shekarun baya da aka yi, sun kuma yi alkawarin tsayawa kai da fata wajen ci gaba da wayar da kan al’umarsu domin tabbatar da kowane yaro kasa da shekara daya an yi masa rijistar haihuwar a yankunansu.


