
Fitaccen jarumin finafinan masana’antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya.
Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da “ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya.”
Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da “mutum mai sauƙin kai” ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya.
Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya fito a finafinai sama da 300 a gomman shekaru da ya yi a masana’antar.
An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1935 a ƙauyen Nasrali da ke lardin Punjab Ludhiana. Malaminsa a makaranta ne ya saka masa suna Dharam Singh Deol.
A tattaunawarsa da BBC a 2018, ya ce mahaifinsa karatu ya so ya yi, amma shi tun da farko fim yake sha’awa, wanda hakan ya sa ya fi mayar da hankali kan harkar ta nishaɗi, kamar yadda jaridar ta ruwaito a shafinta na Facebook.


