Gwamnatin Katsina ta buɗe makarantun sakandare na jeka ka dawo da ta rufe

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‎
A wata sanarwa da ‎ma’aikatar Ilimi ta fitar dukkan makarantun jeka-ka-dawo na jihar za su ci gaba da gudanar da jarabawar zangon farko kamar yadda aka tsara, duk da jita-jitar da ke yawo kan rufe dukkan makarantun jihar.
‎
‎Rufe makarantun ya shafi makarantun kwana kawai, waɗanda za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai wani lokaci, a matsayin matakin tabbatar da tsaro na ɗalibai da malamai.
‎
‎Ma’aikatar ta buƙaci shugabannin makarantun jeka-ka-dawo da su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin gudanar da jarabawa, tare da roƙon iyaye su nuna kula tare da taimaka wa ’ya’yansu a wannan lokaci.
‎
‎Ma’aikatar ta godewa jama’a bisa haɗin kai da fahimta, tana mai cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da ingantaccen tsaro da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa.

Da wannan umurni ana sa ran makarantun firamare da na sakandaren jeka ka dawo a jihar za su buɗe nan take.
‎

By ukarofi