Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi bakuncin Mataimakin Shugaban Jakadancin Jamhuriyar Jama’ar Sin a Nijeriya, Hon. Zhou Hongyou, wanda ya jagoranci wata tawaga zuwa Fadar Gwamnati ta Kano domin ziyarar ban-girma.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.
Hon. Zhou Hongyou ya ce ziyarar tasa na nuna irin girmamawar da kasar Sin ke yi wa Kano a matsayin daya daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
Ya yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa wajen mayar da hankali kan tsaro da jin daɗin al’umma.
Ya bayyana cewa dangantakar Nijeriya da kasar Sin ta dore cikin ƙarfi da moriyar juna tsawon shekaru sama da 60, tare da kasancewar fiye da kamfanonin Sinawa 100 da ke gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na Nijeriya.
Ya ƙara da cewa Kano na ci gaba da zama cibiyar da ake ganin za ta karɓi ƙarin manyan jarin kasashen waje nan gaba.
A jawabinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbi tawagar tare da nuna godiya bisa dogon zumuncin da ke tsakanin Nijeriya da kasar Sin.
Ya amince da irin gudunmuwar da masu zuba jari na kasar Sin ke bayarwa a fannoni da dama, ciki har da gine-gine, kasuwanci, fasaha, da ci gaban masana’antu.
Gwamnan ya bayyana Kano a matsayin cibiyar tattalin arziki mai ƙarfi a arewacin Nijeriya da ma nahiyar Afirka.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa na ba da fifiko ga tsaro, shugabanci mai maida hankali kan jama’a, da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari daga ƙasashen duniya.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da kudurinsa na ƙara karfafa dangantaka da gwamnatin kasar Sin da bangaren masu zaman kansu.
Ya ce sadarwa, bunƙarar kasuwanci, da haɗin kan al’umma su ne ginshiƙan ci gaban gwamnatinsa.
Ya jaddada cewa jama’a ne ginshiƙin duk wata manufa da gwamnati ke tsara wa, kuma jihar za ta ci gaba da gina dangantaka wacce za ta samar wa al’umma ingantattun abubuwan more rayuwa da amfaninsu kai tsaye.
