Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka.
ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayaƙan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya.
An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar.
Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri, ko kuma yunƙurin tserewa.
